Har yanzu Najeriya bata fara sarrafa maganin kanjamau ba – COCSHAN

0

Shugaban kungiyar kare hakin masu dauke da cutar kanjamau na Najeriya (COCSHAN) Ikenna Nwakamma ya bayyana cewa har yanzu kamfanonin sarrafa magunguna a Najeriya basu fara sarrafa maganin cutar kanjamau ba.

Ikenna ya ce babban dalili kuwa shine rashin samun izinin sarrafa maganin daga humumomin gwamnati da abin ya rataya a kan su.

“Sarrafa wannan magani zai taimaka wa gwamnati wajen kula da masu fama da wannan cuta yadda ya kamata.

Ya ce kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje sun fara barazanar daina tallafa wa fannin kiwon lafiyar Najeriya.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne Mohammed Farouk, daya daga cikin wasu sojoji 30 da aka tabbatar sun kamu da cutar Kanjamau bayan dawowa daga aikin samar da zamar Lafiya na rundunar ECOMOG, ya karyata Dokta Jeremiah Abalaka da ya rika cewa ya na da maganin warkar da cutar.

Farouk ya ce a shekarar 1999 zuwa 2000 Dakta Abalaka ya fito ya rika cewa wai yana da maganin warkar da Kanjamau. Tun bayan fadin haka sai hukumar Rundunar Sojin Najeriya ta kwashe su, su 30 aka mika wa Dakta Abalaka domin yayi musu magani.

Farouk ya kara da cewa wannan likita da yake kiran kansa mai maganin Kanjamau, wato Abalaka shirga karya yake ta yi wa mutane. Kashe mutane kawai yake yi da sunan wai yana yi musu magani.

Share.

game da Author