Hada hannu da kungiyar NURTW ya taimaka wajen rage mace-macen mata da yara – Gwamna Bagudu

0

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya bayyana cewa hada hannu da gwamnatin jihar tayi da kungiyar direbobi na NURTW ya taimaka wajen rage mace-macen yara da mata a jihar.

Gwamnati ta hada hannu da kungiyar NURTW ne domin taimakawa wajen daukan mata masu ciki da yara kanana zuwa asibiti idan hakan ya taso cikin gaggawa.

Shugaban kungiyar na kasa Ibikunle Baruwa ya yi kira ga shugabanin kungiyar da su rika yin shugabancin da zai zama abin koyi ga mabiyansu da sauran mutanen a jihar.

Idan ba a manta ba a shekaran 2018 ne asusun Kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya bayyana cewa kashi 55 bisa 100 na jarirai 1000 da ake haihuwa a jihar Kebbi na mutuwa a duk wata.

An gano haka ne bayan gudanar da binciken da hukumar ta yi a Najeriya tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.

Share.

game da Author