Gwammatin Tarayyà ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta fara sayar da gidaje a fadin kasar nan.
Ministan Ayyuka da Gidaje ne, Babatunde Fashola ya bayyana haka, a Legas, a wurin taron masana harkokin manyan gidaje da aka gudanar a Lagos.
Sai dai kuma Fashola bai bayyana farashin kowane gida ba. Sannan kuma bai bayyana adadin gidajen da gwamnatin tarayya za ta sayar a kowace jihar ba.
Sai zai kawai karin bayanin da ya yi shi ne cewa za a saida fam na neman sayen gidajen a online’, inda duk mai bukata zai shiga ya ga karin bayanin komai.
Fashola ya ce idan aka bi wannan tsaro na ‘online’ to wasu ba za su iya yin cuwa-cuwa da gada-gada wajen sayar da gidajen ba.
Ya kuma yi kira ga gwamnoni su bayar da dama ga masu zuba jari a harkar gina gidaje domin su mallaki filayen gini.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta sanar da shirya gina gidaje kimanin 2,000 a wannan shekara, yayin da kasar nan kuma ta na bukatar akalla gidaje 700,000 a kowace shekara, domin rage karancin muhalli.
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa akwai bukatar gidaje milyan 17 a kasar nan kamar yadda Babban Bankin Duniya ya kiyasta.
Bankin kuma ya kara da cewa ana samun karuwar kusan kashi 20 bisa 100 na adadin a duk shekara.
Domin rage wannan wawakeken gibin matsalar muhalli ce Babban Bankin Duniya ya bukaci akalla ba akasara ba, Najeriya ta rika gina gidaje 700,000 a kowace shekara. “Domin magance yawan al’ummar da ba su da nuhalli da kuma kiyayewa daga yin kaura daga karkara ana shiga birane.”
Amma kuma duk da wannan, Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Kasa, ta bayyana shirin gina gidaje 2,383 a cikin wannan shekara ta 2017, maimakon 700,000.
Za a gina wadannan gidaje 2,383 a fadin jihohin kasar nan baki daya, har da Abuja.
Daftarin shirin gidajen dai Ministan Ayyuka da Gidaje ne, Babatunde Fashola ya gabatar da shi a lokacin da ya ke jawabi a gaban Kwamitin Gidaje da Ayyuka na Majalisar Dattawa.
Ya zuwa cikin watan Satumban da ya gabata, har ma an damka wa ma’aikatar naira bilyan 19.8 domin wannan aiki.
Sai dai kuma ya ce akwai ayyukan da ba a biya ba na baya, tun daga shekarar 2001 zuwa 2017 da suka kai naira bilyan 78.2.
Babban Bankin Duniya dai a rahoton sa na karshen 2018, ya ce babban cikas din da Najeriya ke samu wajen kasa samar da wadatattun muhalli su ne filayen gina gidaje, rashin kayan inganta rayuwa, samun iznin gini, tsadar kayan gini da sauran su.
Fashola ya kara da cewa ma’aikatar sa na bakin kokarin ganin an kammala gine-ginen da ake yi a sakateriyar gwamnatin tarayya ta jihar Anambra, Bayelsa, Ekiti, Nasarawa, Osun da ta Zamfara.
Discussion about this post