Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta yi kwakkwaran kira ga Gwamnatin Jihar Sokoto ta haramta wa masu tallar magungunan gargajita yin furucin batsa da kuma baza hotunan batsa a fadin jihar.
Wannan wani kudirin gaggawa ne da Shugaban Kwamitin Harkokin Lafiya, Ibrahim Sarki ya gabatar a zauren majalisar jiya Alhamis.
Sarki shi ne dan majalisar da ke wakiltar Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa, a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya ce irin yadda masu tallar maganin gargajiya ke cire kunyar jama’a a idon su, su na amfani da kalamai na batsa da kuma hotunan batsa wajen tallar magunguna, abin damuwa ne matuka.
“A koda yaushe su na furuci na kalaman batsa da kuwa barbaza hotunan batsa, wadanda hanya ce mai koya wa yara bin hanya karkatacciyar da tarbiyar su za ta gurbace.
“Irin yadda suke tallar magungunan su ya saba wa al’adar mu da addinin mu da kula dabi’ar mu. Don haka karya doka ce karara su ke yi.
“Sannan kuma su na amfani da kananan yara masu sayar musu da wannan magunguna, ta hanyar yin amfani da lasifika mai kara sosai a kan manyan titina.
Daga nan sai ya yi kira da cewa ya kamata gwamnatin ta gaggauta haramta masu irin wadannan sana’a.
Duk dan majalisar da ya yi magana dai babu wanda bai kushe irin tsarin tallar masu saida magungunan gargajiyar ba.
Mataimakin Kakakin Majalisa, Abubakar Magaji, wanda shi ya jagoranci zaman majalisar, ya sa an kada kuri’ar amincewa ko kuma rashin amincewa.
Wadanda suka amince a kafa dokar ne suka yi rinjaye mai yawan gaske.