Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS), Babatunde Fowler, ya bayanna cewa nan da watan Disamba Najeriya za ta kammala tattara sunayen mutane miliyan 45 da za ta rika karbar haraji a hannun su.
Fowler ya yi wannan kalami ne yau Alhamis a garin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara. Ya yi bayanin a wurin kaddamar da Shirin Amfanin da Lambonin Tantance Masu Biyan Haraji (Tax Identification Number).
An fara kaddamar da shirin a Shiyyar Arewa ta Tsakiya, a Ilorin. A wurin, Fowler ya ce shekaru hudu na wannan gwamnatin a bada karfi sosai wajen inganta karfin tattalin arziki. Kuma wannan kokari ya na cimma ruwa a gimin da a ke yi.
“Farkon hawan wannan gwamnati, wadanda ake karbar haraji a wurin su ba su wuce mutane milyan 10 ba. Da tafiya ta mika, har ta kai mu na kadba ga mutane milyan 20.
“To a yanzu kuma shiri ya kammala yadda nan zuwa karshen watan Disamba za mu kai ga karin mutane milyan 25, sun zama milyan 45 kenan.”
Ya ce kowa zai samu lambar shaidar tantance cewa zai rika biyan haraji. Wannan lamba dai kamar lambar sa-idon gwamnati ce a kan asusun ajiya na bankuna, wato BVN.
Daga nan Fowler ya rika bada bayanin cewa irin nasarorin da ya samu wajen tara makudan kudaden harajin cikin gida, a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Idan ba a manta ba, Shugaba Buhari ya nemi a samo hanyoyin kudaden shiga wadanda rika amfani da kudaden ana biyan karin albashin ma’aikata, wanda har yau maganar fara aiki da karin ta ki ci, ta ki cinyewa.