Gwamnatin Najeriya ta kara nanata matsayin ta wajen hukunta kangararrun da ke yada labaran karya ko na nuna kiyayya a kasar nan.
Sai dai kuma a cikin kasar mutane da dama na sukar gwamnatin cewa maye-fake-da-annoba ta ke so ta yi, domin ta dakile ‘yancan fadar albarkacin bakin jama’a ta hanyar yi wa kafafen yada labarai takunkumi.
Ana tsare da wasu ‘yan jarida, masu rajin kare jama’a da kuma wasu da ake ci gaba da tuhumar su a kotuna daban-daban a bisa zarge-zargen tayar da husuma, kokarin kifar da gwamnati da sauran su.
Wasu da ake tsare da su, har da Shugaban Jarida Sahara Reporters, Omoyele Sowore da Agba Jalingo wanda shi kuma ake tsare da shi Cross River.
Amma kuma a haka din gwamnati ta ce za ta fara yi wa masu yada labaran karya da na kiyayya dirar mikiya.
Ministan Yada Labarai ne, Lai Mohammed ya ce babu wani korafi ko suka ko kulle-kulle da zai sa gwamnati ta fasa fito da dokokin murde wuyan kafafe da masu yada labaran karya da na kiyayya.
Lai ya fadi haka ne a ranar Lahadin da ta gabata, a wani taro da ya yi da masu kafafen yada labarai na online a Lagos.
Babu wanda zai kushe wannan kyakkyawan tsari sai wanda ba ya kishin Najeriya da ‘yan barababiya wadanda ba su yabon abin alheri sai yayata na sharri.
“Wanda duk ku ka ga ya tsargu, to shi ne ya san ba shi da gaskiya. Masu yada labarai na gaskiya ai ba su da wata matsala, shi ya sa ba su damu ba.” Inji Lai.
Lai ya ce ba takunkumi ko tauye ‘yancin kafafen yada labarai za a yi ba. Baragurgi ne dai za a karkade.