Wani Likita da ya kware kan ilimin sanin amfanin sinadarorin dake cikin ganyayyaki Paul Okoh ya yi kira ga mutane da su yawaita cin ganyen lansuru cewa ganyen na dauke da sinadarorin dake hana sa kamu da cututtuka sannan da kara karfin garkuwar jiki.
Dakta Okoh yace ganyen lansuru na dauke da sinadarin ‘Beta-carotene da Vitamin C’ wanda ke taimakawa wajen warkar da ciwo a jiki, ciwon sanyin kashi ‘Arthritis’, daji da sauran su.
Akan hada ganyen lansur a cikin abinci kamar shinkafa, faten dankali, faten tsaki da kuma sauran su sannan aka ci wannan ganye danye ko kuma a kwadanta shi da kuma garin kuli-kuli wanda likitoci suka ce yin haka ya fi karfafa garkuwan jiki.
Ga sauran amfani 15 da ganyen lansuru yake da shi
1. Cin Ganyan lansuru na maganin ciwon ido
2. Yana maganin hawan jini.
3. Cin ganyen lansur na gyara fatar mutum. Lansuru na maganin Kyasfi dake kama fata. Ana nika shi a hada da man da ake shafawa ko kuma da ruwa a shafa a jiki. Yana gyara fata sosai.
4. Yana taimaka wa mutum cin abinci yadda ya kamata.
5. Yana maganin ciwon ciki kamar zawo da sauransu.
6. Ganyen na kawar da ciwon zuciya.
7. Yana tsaida amai. Idan mutum yana yawan jin amai, lansuru na maganin shi.
8. Yana kara karfin kashi.
9. Yana kara karfin namiji.
10. Cin Ganyen lansur na kawar da warin baki.
11. Cin ganyen Lansuru na kawar da laulayin da mata kan ji idan suna jinin al’ada.
12. Yana rage kiba a jiki.
13. Yana warkar da rauni ko ciwo a jikin mutum.
14. Yana kawar da ciwon siga.
15. Yana kara jini.