Da Sunan Allah, Mai Yawan Rahama, Mai Yawan Jin kai
Gaisuwa da yabo su kara tabbata ga Manzon Allah (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa da duk wadanda suka bi su da kyautatawa baki daya har zuwa ranar sakamako.
Ya ku ‘yan uwa masu albarka, za ku yi mamakin bude wannan rubutu nawa na yau da wannan magana ta masu hikima, wato ‘FITINA BACCI TA KE YI, ALLAH YA LA’ANCI MAI TA DA ITA.’ Wannan magana nasan ba Hadisi ba ne, amma magana ce ta masana, masu hikima da dukkannin mu mun yarda da ita, kuma jarabawa ta tabbatar da kasancewar wannan magana gaskiya. Mutane suna yawan fadar wannan magana ga mutanen da ke kokarin tayar da fitina a cikin al’ummah, lokacin da ake zaune lafiya ko kuma lokacin da aka fara samun zaman lafiya bayan barkewar rikice-rikice da ke addabar al’ummar.
Ya ku bayin Allah, ya ku Kanawa da dukkanin ‘yan Najeriya, sanin kan ku ne, bayan barkewar rikici tsakanin masarautar Kano da gwamnatin Jihar Kano, wanda dukkanin Musulmi mai imani, yana kallon wannan rikici a matsayin wata kaddara daga Allah Subhanahu wa Ta’ala, da ta riga fata, wadda ba’a iya kauce ma wa dole sai ta auku. Bayan daukar lokuta masu tsawo ana kai ruwa rana tsakanin bangaroran guda biyu, wanda bai haifarwa Kanawa da al’ummah komai ba illa ci baya da rashin hadin kai.
Ana cikin wannan ne, Allah cikin ikon sa, da iyawar sa, ba tare da wayon wani mutum ko dabarar sa ba, Allah ya fara zuba wa wannan rikici ruwa, ya fara lafawa, aka fara hangen sa’ida, bayan gwamnan Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya kai wa Mai Martaba Sarki wata ziyara a masaukinsa da ke babban birnin tarayya, wato Abuja. Wanda daga bisani shi ma Mai Martaban ya kai wa Gwamna Ganduje irin wannan ziyara a gidan gwamnatin Jihar Kano. Wadannan ziyarce-ziyarce, Allah ya sani, dukkan wani Bakanon asali, ba bakon haure ba, da dukkanin wani dan arewa mai kishin arewar da gaske, sun yi farin ciki da murna da su, domin har suna ta yin addu’o’i da fatan Allah yasa wannan al’amari ya dore, domin a samu zaman lafiya, musamman a Jihar Kano da ma arewa baki daya.
Ashe wannan al’amari sam bai yi wa wasu dadi ba, suna ganin yin sulhu kamar barewar miyar gidan su ne. Suna ganin su fa wannan rikici shine cin su, kuma shine shan su. Saboda haka sai suka sha alwashin cewa, su fa idan suna raye, to ba za su taba bari a samu zaman lafiya tsakanin masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano ba. Daya daga cikin wadannan mutane kuwa shine Fa’izu Alfindiki, wannan mutum yana daga cikin magoya bayan Gwamna Ganduje, kuma yana cikin masu bai wa Gwamnan shawara. Duk mai bibiyar wannan mutum da rubuce-rubucen sa a kafafen sadarwa na zamani, wallahi zai tabbatar da abun da na fada, kuma zai yarda da ni dari-bisa-dari, sannan zai yi imani da Allah cewa, wannan mutum yana daga cikin makiyan Kanawa kuma makiyan arewa, wadanda ba su son zaman lafiyar wannan yanki. Kuma ba domin komai ba sai don dan abinda suke samu na sa wa aljihu da bakin salati.
Kira na ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya sani cewa wannan mutum sam wallahi ba ya nufin sa da dukkan Kanawa da alkhairi. Don haka yasan matakin da zai dauka a kan sa, domin ba ya da aiki sai kara tarawa Gwamna makiya kullun safiya, alhali a matsayin Gwamna Ganduje dan siyasa, jama’ah yake nema.
Duk wata karya da sharri da ake yadawa domin kara rura wutar rikici tsakanin masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano, wannan mutum Alfindiki, wallahi yana cikin masu yada ta. Don haka, wallahi, ina kira ga ‘yan uwa na, Kanawa masu albarka, da suyi taka-tsan-tsan da wannan mutum, kuma su sa masa ido, kuma su yi hankali da shi kar ya jefa Jihar Kano cikin rikici, Allah ya kiyaye, amin.
Ya ku jama’ah, eh, wallahi da gaske ne, ni ba dan Jihar Kano ba ne, amma tsakanina da Allah, Allah ya sa man kaunar Jihar Kano da Kanawa baki daya, watakila ma fiye da wasu Kanawan, wanda a halin yanzu, daga Jiha ta ta Zamfara babu inda ni ke so in zauna in rayu kamar Kano. Wannan ina fada ne har zuci, kuma na san Allah masani ne akan abinda ke cikin zukatan bayin sa, idan ba da gaske ni ke fada ba Allah ya sani! Shi yasa kuka ga bana daga kafa akan duk wani mutum mai kokarin ruguza Kano da zaman lafiyar ta.
Don haka nayi wannan rubutu ne saboda Gwamna ya sani, Kanawa su sani, jami’an tsaro su sani, kai dukkan wani mutum mai kishin Kano da arewa su sani cewa, ga fa wadanda suke rura wutar rikici a cikin al’ummah, wadanda basu kaunar a samu zaman lafiya. Sannan mun san cewa wannan Gwamnatin tana ikirarin fada da masu yada kalaman batanci a cikin al’ummah, don haka su san abinda wannan mutum yake yi na yada fitina a cikin jama’ah.
Duk wani sharri, makirci, shaci-fadi, soki-burutsu da karya da ake yadawa game da badakalar Maja Sirdin Sarkin Kano, wannan mutum yana daga cikin masu yada ta, yana daga cikin mutanen da ke shiga kafafen yada labarai na zamani suna rubuta karya, don karancin imani da rashin tsoron Allah, saboda kawai ya kara samun shiga a wurin Gwamna da magoya bayan sa.
Bayan da wannan mutum da ire-iren sa suka fahimci cewa duk wata karya da suka yada, suka yiwa masarautar Kano kage, wai cewa an kori Maja Sirdin Sarki saboda ya tarbi gwamna Ganduje, bai yi tasiri ba, yanzu sai suka kulla wata makarkashiya da wani sabon sharrin. Suka dauki shi Alhaji Auwalu, wato shi Maja Sirdin, wanda duk akan sa ne ake son a yada barna da sharri, suka dauki nauyin sa, ya tafi yayi fira da gidan rediyo, cewa wai lallai gaskiya ne an kore shi. Alhali masarautar Kano ta fito ta sanar da duniya cewa, wannan al’amari fa ba gaskiya ba ne. Idan kuma har yace an kore shi, to ya kawo takardar shaidar korar ta sa, kamar yadda aka ba shi takardar daukar sa aiki. Sannan ya fada waye ya kore shi?
Wannan fira da suka dauki nauyi aka yi da shi, tana nan yanzu haka miyagu suna yada wa a kafafen yada labarai, domin ida manufa ta sharri.
Ya ku jama’ah, kun san sharri irin na shaidan, shi yanzu wannan Alhaji Auwalun fa, wai shine masu adawa da masarautar Kano suke ta zawarci a halin yanzu. Domin da ma can kun san halin su sarai, duk wanda suka san ya samu matsala da masarauta, sanadiyyar laifin da shi kan sa ya aikata, sai ka ga sun jawo shi a jiki don yin amfani da shi. Wannan tsakanina da Allah, Mahalicci na, shine abinda yake faruwa a Jihar Kano, don haka wallahi sai mun kiyaye! Shi kuma Alhaji Auwalun ya yarda din suyi amfani da shi, saboda hangen abinda za su bashi, na duniya mai karewa. Shi yasa ya yarda ya biye masu, ya tafi har gidan rediyo aka yi fira da shi, ya fadi karairayi, suka dauki nauyi, don su yada, wai da nufin su sa masarautar Kano tayi bakin jini. Sun manta da cewa shi farin jini daga Allah ne, kuma shine yake ba wanda yaso daga cikin bayin sa, kuma yanzu ya bai wa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, don haka wallahi kun makara!
Bayan haka, ya ku ‘yan uwa, nayi kokarin gabatar da wannan bayani ne zuwa ga re ku saboda ganin yadda na lura cewa, wasu daga cikin mutane sun sa kan su cikin wannan mummunan dabi’a ta yada husuma a cikin al’ummah, da fatan Allah zai amfanar damu da wannan bayani, domin mu gane, mu kauce wa wannan mummunan aiki.
Yada husuma a cikin al’ummah a shari’ance yana nufin mutum ya dauki maganar wani ya kaiwa wani, ko yayi wani rubutu da nufin hada husuma a tsakaninsu, ko cutarwa; ko kuma yada karya a cikin al’ummah da nufin hada rikici ko husuma.
Kuma kamar yadda muka sani, wannan aiki haramun ne, da nassin Alkur’ani da Hadisan Shugaba Annabi Muhammad (SAW), sannan kuma yana daga cikin manyan zunubai.
Daga cikin dalilan da ke nuna haramcin yin haka, akwai fadin Allah (SWT) cikin littafinsa mai tsarki cewa:
“Mai yawan aibata mutane, mai yawan yada gulma (tsakanin mutane).”
Da kuma fadin Allah Madaukaki cewa:
“Shin dayan ku yana so ya rika cin naman dan uwan sa alhali yana mushe? To kun kyamaci haka… [Hujurat: 12]
Sannan kuma Manzon Allah (SAW) yace:
“Dukkan mutum Annamimi, mai gulma, mai hada husuma tsakanin mutane ba zai shiga Aljannah ba.” [Buhari da Muslim]
Sannan wata rana Manzon Allah (SAW) ya wuce wasu kaburbura guda biyu, sai yace yanzu haka ana yiwa mutanen da ke cikin kaburburan nan azaba. Kuma su a wurin su, ba wani babban laifi suka yi ba, daya daga cikin su ya kasance idan yayi fitsari ba ya tsarkaka da kyau daga fitsarin, wato idan ya gama fitsari baya bari ya gama digewa gaba dayan sa. Na biyun kuma ya kasance mai yawan yawo tsakanin mutane yana yada annamimanci da husuma tsakanin su. [Buhari da Muslim ne suka ruwaito]
Sannan Manzon Allah (SAW) yace:
“Zaka samu daga cikin mafiya sharri a cikin mutane, sune masu fuska biyu wadanda zasu zo wa wadannan mutane da wata fuska sannan su je wa wadannan da wata fuskar.” [Buhari da Muslim ne suka rawaito]
Har ila yau Manzon Allah (SAW) yace:
“Dukkan wanda ya kasance yana da harshe biyu a gidan duniya (wato mai hada husuma) to Allah zai sa masa harshe biyu na wuta a ranar Alkiyama.” [Abu Dawuda ne ya rawaito]
Sannan Ka’ab yana cewa:
“Ku tsoraci annamimanci da hada husuma cikin al’ummah, domin ma’abucin wannan baya hutawa daga azabar kabari.”
Mansur ya ruwaito daga Mujahid dangane da matar Abi Lahab wadda asalin sunanta Arwa, sannan ana mata Alkunya da Ummu Jamilah, inda Allah Madaukaki yake fada game da ita, cewa:
“Da matarsa ina nufin magulmaciya.” [Suratul Masad]
Wannan mata mummuna ce, mai ido daya, amma ba abin da ta ke yi sai zunden Manzon Allah (SAW), da yi masa sharri da karya, da tsara baitocin waka domin keta alfarmar sa, da cin mutuncin sa (SAW), tare kuma da kokarin hada husuma tsakanin al’ummar Musulmi.
An ruwaito cewa wata rana wani mutum ya je wurin Umar Ibn Abdul’aziz ya kai masa gulmar wani mutum da nufin hada husuma, sai umar Ibn Abdul’aziz yace masa:
“Ya kai wannan mutum idan na ga dama zan duba lamarin ka, idan ka kasance mai gaskiya, to kana daga cikin wadanda Allah yake cewa: “Idan fasiki yazo maku da wani zance to ku yi bincike…” [Suratul Hujurat:6 ) Idan kuma ka kasance makaryaci, to kana daga cikin wadanda Allah yake fada a kan su cewa: “Mai yawan aibata mutane, mai yada gulma.” (tsakanin mutane) [Suratul Kalam: 11] Idan na ga dama in yafe maka, sai wannan mutum yace: ka yafe mani ya Sarkin muminai, bazan sake aikata haka ba.”
Wani mutum yazo wurin Aliyu Dan Husain (RA) yace masa:
“Wane ya zage ka, kuma yace da kai kaza da kaza, sai yace: zan tafi wurin sa, sai suka tafi wurin sa tare da tsammanin zai tafi ne ya kare kan sa; lokacin da suka isa wurin sa, sai yace: Ya dan uwa na, idan abin da ka fada game da ni gaskiya ne, to Allah ya gafarta mani, idan kuma abin da ka fada game da ni ba gaskiya ba ne, to Allah ya gafarta maka.”
Ya ku ‘yan uwa, ga abubuwan da ya kamata mu aikata a duk lokacin da irin wadannan miyagun mutane masu yada husuma a cikin al’ummah suka zo muna da labaran kanzon kurege, na karya da suke yada wa domin cimma wani buri na su na sharri, kamar haka:
1. Kada ka gaskata labarin da aka zo maka da shi, domin wanda yazo da labarin ya zama Annamimi, fasiki, kuma mai mayar da alheri.
2. Ka hana wanda ya kawo maka wannan labarin ci gaba da yada wannan labarin ta ko wane hali, kuma kayi masa nasiha sannan ka kyamaci aikata hakan.
3. Ka nuna masa kai fa kana jin haushin sa domin Allah, don Allah yana fushi da aikin da yake yi, kuma yin fushi domin Allah wajibi ne.
4. kada kayi mummunar zato dangane da wanda aka kawo maka gulmar sa, domin Allah (SWT) yace:
“Ku nisanci mafi yawa daga cikin zato…” [Hujurat:12]
5. Kada mutun yace zai yi bincike don gano abin da aka fada masa, karya ce ko gaskiya ne, domin Allah (SWT) yace:
“Kuma kada kuyi wa juna binciken kwakwaf…” [Hujurat:12]
6. Kada mutum yaci gaba da labartawa wasu abin da aka kawo masa na gulma ko wanda aka rubuta, domin idan yayi haka, shima sai ya koma matsayin wanda yazo masa da gulman.
Bayin Allah, wadannan sune kadan daga bayanai da nayi niyyar yi, domin fadakar da kaina da ‘yan uwa na hadarin wadannan mutane masu yada husuma tsakanin al’ummah, da fatan Allah ya kare mu daga aikata wannan mummunan dabi’a, ya shirye mu da dukkan Musulmi baki daya, amin.
Wassalamu alaikum warahmatullah wa bara ka tuhu.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma: 08038289761.
Discussion about this post