Fitattun ’yan kwallo 11 da suka buwayi duniya daga 2010 zuwa 2019

0

Yayin da shekarar 2020 ke gabatowa, mashahuriyar jaridar ‘online’ ta kwallon kafa ta duniya, wato Goal.com ta gudanar zaben tantance mashahuran ‘yan wasa 11 wadanda suka fi saura taka rawa a lambar da kowanen su ke bugawa a duniya, cikin shekaru 10. Wato tsakanin 2010 zuwa karshen 2019.

Kwararrun marubuta labaran wasanni su uku, Peter Staunton, Stefen Coerts da Sam Brown ne alkalan kwamitin tantance zakakuran ‘yan wasan 11.

Sun bi hanyoyi biyu wajen fitar da wadanda suka fi saura shahara da taka rawa a lambar da kowanen su ke bugawa.

Hanyoyin su ne irin nasarar da dan wasa ya samar wa kungiyar sa, sai kuma wadda ya samar wa kasar sa a duniya baki daya.

MAI TSARON GIDA: Manuel Neuer (Maganadisun Kwallo)

Duk da cewa kakar wasanni kusan biyu da su ka gabata, Manuel Neuer ya sha fama da jiyyar ciwuka ko raunukan da ya ji a wurin wasa, duk da haka babu wani mai tsaron gida a tsawon shekarun nan 10 da zai iya bugun kirji a gaban sa.

Kada ma a kai ta da nisa Hukumar Kididdigar Tarihin Kwallon Kafa ta Duniya (IFFHS) ta jera shekaru 4 a jere tsakanin 2013 zuwa 2016, ta na ba shi gwarzon mai tsaron gida na duniya.

Baya ga rawar da ya taka a kungiyar Beryen Munich tsawon shekaru, inda kulob din ya buwayi sauran kungiyoyi, Nuer ya taka rawa wajen cin kofin Kwallon Duniya a 2014.

Wannan gwanin mai tsaron gida, na kan kwantar wa ‘yan kallo da kociya hankali, domin an camfa shi cewa ko an wuce sauran masu tsaron baya, to jefa kwallo a raga,

‘sai dubu ta taru.’

LAMBA 2: Dani Alves (Mummuna da Aiki)

Duk inda ake neman dan baya na gefan dama, wato lamba uku, idan aka samu Dani Alves, to shikenan. An dade ba a yi irin sa ba, kuma a kullum ya na tabbatar da shi gwani ne wajen tare mahara zuwa kai farmaki, samame ko atisaye.

Dani Alves ya ci kofi a Spain, Italy, France da Champions Lague biyu a Barcelona.

Ya shafe shekaru goma ya na buwayar ‘yan gaba na duniya, sannan kuma idan ta yi daga-daga ya na haurawa sama ya bar kofar gidan sa a bude, ya je ya taya mahara kai hari. Sannan ya dawo a guje ya rufe kofar gidan sa, ba tare da an samu baraka ba.

Alves ya ci kofuka kusan 40 a kulob-kulob da kuma kasar sa, Brazil.

LAMBA 6: Raphael Varane (Raina Kama Ka Ga Gayya)

Har yanzu Raphael Varane yaro ne dan shekaru 26. Amma yanzu haka ya shafe shekaru 8 cur ya na taka rawa a kungiyar Real Madrid. A wannan lokacin ya ci kofin La Liga sau biyu, kuma ya ci Champions League har sau hudu.

Ya yi kokari kwarai wajen lashe Kofin Duniya da Faransa ta yi a Rasha, cikin 2018.

Inda ya kware shi ne wajen iya natsuwa da tsayawa tsayin daka ya hana dan gaba wucewa ko kuma kwace kwallo ko tare da daga kowane hatsabibin dan wasan da duniya ke tinkaho da shi. Abin birgewa ga Varane shi ne, yadda ya ke cika-aiki ba tare da yawan ya jangwalo laifin da alkalin wasa ke rika yawan hura masa usur ba.

LAMBA 5: Sergio Ramos (Mugu sai Allah-ya-isa)

Ko tantama babu, Sergio Ramos ya yi suna biyu a duniyar kwallo. Sunan farko shi ne ya iya aikin sa na tsaron baya. Kuma duk duniya kowa ya shaida haka, har ma wanda ba ya sha’awar kwallo. Na biyu kuma ya yi kaurin suna wajen iya keta. Ita ma duk duniya kowa ya shaida, har wanda ba ya sha’awar kwallon kafa. Dogo ne, kakkarfa, amma kuma maguji ne, wanda ba ya jin nauyin jikin sa.

Yaro ko da me ka zo, Ramos ya fi ka. Yay i kaurin suna kuma wajen cin kwallaye da kai a daidai kusa da lokacin da alkalin wasa ke niyyar hura tashi.

Idan ka fi shi iya wasa da kwallo, shi kuma ya fi ka rashin imanin rafke ka kasa, ka ji ciwo, a fitar da kai, kowa ya huta.

Shekaru 15 kenan Ramos na jan zaren sa, har yau bai tsinke ba. Shi ne dan wasan da aka fi tsana a duniya, duk kuwa da cewa masoyan sa ma ba a fi su yawa ba.

Da yanzu a ce wane dan wasa daya tal ne Real Madrid, to tabbas Sergio Ramos za a nuna, a ce wancan ‘shegen’ ko wancan ‘mugun’. Ramos kenan. Ana son ka, kuma ana kushe ka.

Ya ci kofin Champions League a Real Madrid har sau hudu, kuma ya taimaki Spaian ta ci Kofi Duniya cikin 2010.

Har yau kungiyar da ta raine shi wato Sevilla na jin haushin barin kulob din da ya yi. Magoya bayan kungiyar kuwa, har gobe babu dan wasan da suka tsana a duniya kamar Ramos.

LAMBA 3: Marcelo (Gajere Kusar Yaki)

Ba a yi dan baya na gefen hagu kamar Marcelo ba a tsakanin 2014 zuwa 2018. Za a iya cewa kusan rawar da Cristiano Ronaldo, Sergio Ramos, Gareth Bale da Luka Modric suka bayar a cin kofin Champions League hudu da suka yi a Real Madrid, to shi ma Marcelo irin ta ya bayar a cikin wadancan shekaru biyar.

Irin yadda ya ke wasa, tare ‘yan gaba da kuma taya mahara kai kai hari da farmaki da atisaye, har ma da jefa kwallo, ta sa Marcelo ya na da farin jini ga magoya bayan Real Madrid, Zinedine Zidane, Ronaldo da kuma ‘yan kasar Brazil.

TSAKIYA: Toni Kroos (Kada Dama Ruwa)

Toni Kroos na daya daga cikin wadanda kwallo ta aura a cikin shekarun nan 10. Ya yi rashin sa’a ya na cikin gwanaye a cikin Real Madrid da kuma kasar su ta Jamus, shi ya sa ko an yi nasara, ba a cika ganin gudummawar sa kuru-kuru ba.

Amma dai dan wasan da ke karbo kwallo daga wurin ‘yan baya ya na raba wa ‘yan gaba, har a yi nasarar cin kofin Duniya da kuma Champions League har hudu, to ba kasheshe ba ne, rodi ne.

A cikin 2013 da shi Bayern Munich ta lashe kofi uku a kakar wasa daya. Da shi Jamus ta ci Kofin Duniya, kuma da shi Real Madrid ta buwayi duniya cikin shekaru hudu a jere.

Kroos ya shigo da sabon salon wasa a Madrid, ga shi kuma arha takyaf aka saye shi, fam milyan 25 kacal.

CM: Sergio Busquets (Dakaren yakin Galatico da El-Clasico)

Watakila saboda a duk lokacin da Barcelona ta kai maza a kasa, Sergio Busquets bai cika fitowa ya na kururuwar samun nasara da cika-baki kamar sauran ba, shi ya sa ba a cika kula da irin nasarar da ya ke taimakawa ana samu ba.

Amma dai a cikin shekaru 10 Busquets ya taimaka wa Barcelona cin kofi 7 na La Liga, da Champions League biyu.

Busquets ya ci Kofin Duniya da kasar sa Spain ta yi nasara kuma ya ci Kofin Turai duk da Spain.

TSAKIYA: David Silva ( Wukar yanka giwa….)

Hausawa dai na cewa wukar yanka giwa, mai kaifi ake bukata ba mai girma ba. To wannan magana ta yi daidai da David Silva, wanda tun bayan komawar sa Manchester City cikin 2010 daga Valencia, ya zamo karfen kafa da alakakai ga dukkan kungiyoyin wasan Premier League na Ingila.

Ya kasance abin yabo daga Pep Guardiola a ko da yaushe. Har ma ya na cewa Silva na daya daga cikin ‘yan wasa masu amfani da kwakwalwar su da ya fi sani a duniya. Silva ya taimaka wa Manchester ta ci kofi hudu a cikin wadannan shekaru.

LAMBA 10: Lionel Messi (Wanda ya iya ya huta)

Bari mu ari irin kirarin da Dan Anace ya yi wa Shago, mu yi wa Messi. Duk wanda bai ga kwallon Messi ba, to ya na da sauran kallo. “Ya dai zaka duniya kamar bai zo ba…”

Mashahurin mai tsaron gidan kungiyar Juventus, wato Gianluigi Buffon, ya taba cewa: “tsakani da Allah Messi wata irin halitta ce daga wata duniya, amma ya zo wannan duniyar ya na buga kwallo tare da mu ‘yan Adam.”

Duk yadda z aka fassara Messi, ba za ka kai yadda Buffon ya fassara shi ba. Sai dai kawai a rufe shafin sa da ce masa gwani na gwanaye kawai.

Cikin shekaru 10 kadai Messi ya na kwallaye 779 wadanda ya ci da kuma wadanda ya taimaka aka ci, idan za a yi jimillar su kenan.

Duk da har yau bai ci kofin duniya ba, kuma bai ci wa kasar sa Argentina wani babban kofi ba, al’ummar da ke kallon kwallo na da har ma da na yanzu, sun yi ittifakin cewa ba a taba yin dan wasan da ke lailaya kwallo kamar Messi ba.

LAMBA 9: Robert Lewandowski (Guga ba ki tsoron rami)

Baya ga Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo, babu wani dan wasa na uku da ya ci wa kungiyar sa kwallaye kamar Robert Lewandowski.

Ga shi dogo, sannan kuma ba ya tsoron shiga kowane rimtsi ko karimtsa da rimatson kartin ‘yan baya. Duk yadda kwallo ta same shi a cikin yadi 18, duk yawan masu tsaron baya, Lewandowski zai iya kai kafar sa. Sai dai ka ji ‘yan kallo na ihu kawai, kwallo ta shiga raga –aikin Gama ya gama.

Bayan ya buwayi Bayern a lokacin da ya ke Brussia Dortmund, ya koma Bayern din inda ya rika cin kofuka rututu a kungiyar. An shaida yadda ake yin kare-jini-biri-jini a wasannin da Lewandowsky ke bugawa a Bayern yayin cin kofin Champions League a duniya.

LAMBA 7: Cristiano Ronaldo (Maye ka ci dubu sai ceto)

Wanda ya rasa yadda zai kwatanta Cristiano Ronaldo, to kada ya tsaya dogon tunani. Kawai ya kwatanta shi da jarumin fim din nan na ‘Bahubali’ ko ‘Terminator’, ko kuma irin balbalin bala’in da jarumin ‘The Troy’ ya yi.

Duk wani tarihin da wani dan kwallo ya kafa a duniya, babu wanda Ronaldo bai karya kofar say a wuce ba, sai ‘yan kalilan.

Ronaldo komai ya iya. Ya na cin kwallo da kafar dama, ya na ci da kafar hagu sannan kuma ya na ci da kai. A cikin shekarun nan 10, babu wani dan kwallon da aka fi yawan ambaton sunan sa. Ya fi kowa yawan mabiya a shafin na Instagram a duniya.

Ya fara kafa tarihi a Manchester United, ya bar ta, ya koma Real Madrid, inda a can a cikin shekaru biyar na karshen shekaru tara da ya yi, ya kafa tarihin da ‘yan kwallo ba su kafa ba, kuma ya kankare wa Madrid duk wani miki da bakin cikin da ya buwayi kungiyar tun bayan cin kofin Champions League da kulob din ya yi a 2002.

Za a dade ba a sake yin kamar Ronaldo ba, idan ma har za a sake yi.

Baya ga lashe Gwarzon Dan Kwallon Duniya da na Turai da Ronaldo ya sha yi, ya ci Kofin Champions League sau biyar, kuma ya lashe kofin Turai na 2016.

A yanzu Ronaldo na da kwallaye 699, saura guda tal ya cika 700.

Share.

game da Author