Falake ya bi, ya ce sai Bello a Kogi

0

Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kogi, James Falake ya dawo daga rakiyar adawa da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello inda ya daga hannun gwamnan a zabe mai zuwa.

Idan ba a manta ba, James Falake ne dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kigi a 2015 tare da dan takara marigayi Abubakar Audu.

Sai dai tun bayan rasuwar Audu, jam’iyyar ta mika wa Yahaya Bello kujerar maimakon Falake.

Dalilin haka kuwa Falake ya ki amincewa yayi wa Bello Mataimaki.

Tun a wancan lokaci Falake ya koma jihar Legas inda yake wakiltar mutanen Legas a majalisar Tarayya.

Falake ya bayyana cewa tun bayan wannan lokaci ya koma gefe suna kallon salin mulkin Yahaya Bello.

” Ina so in tabbatar muku cewa mun gamsu matuka da irin salon mulkin Yahaya Bello kuma muna tare da shi dari bisa dari.

” Sannan ku sani abin da Bello yayi ya zarce abin da PDP ta yi tsawon mulkinta a jihar, wato shekaru 16 a baya.

” A matsayina na jigo a jihar Kogi, babu tantama ko kokwanto da nake dashi cewa ba Bello bane zai lashe zaben Kogi.

” A ranar 16 ga watan Nuwamba ne za gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa.

Jam’iyyar APC da PDP duk sun wasa wukaken su domin ganin yan takarar su ne suka lashe zabe.

Share.

game da Author