Faiza ta roki kotu ta raba aurenta da mijinta a Kaduna saboda baya son haihuwa ratatata

0

A ranar Laraba ne wata mata mai suna Faiza Yusuf mai shekaru 27 ta kai karat mijinta Muhammad Abubakar kotun dake Rigasa jihar Kaduna saboda mijin baya son ta kara haihuwa.

Faiza dake zama a unguwar Nasarawa a Kaduna ta bayyanawa kotun cewa mijinta Abubakar baya so ta kara haihuwa bayan ‘ya’ya biyu kacal da suka haihu da shi.

“ Saboda baya son haihuwa Abubakar ya yi mun barazanar musanta ciki na idan har na sake daukan wani ciki.

Faiza ta ce banda haka Abubakar na zarginta da neman maza a waje.

“ A dalilin haka nake rokon kotu ta raba auren mu domin na gaji da irin wannan zama da muke yi.

Sai dai kuma Abubakar bai halarci zaman kotun ba a wannan rana.

Alkalin kotun Attahiru Bamalli ya dage shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Disemba.

Share.

game da Author