Duk wanda ya kara tare min hanya a bindige shi – Gwamnan Ebonyi

0

Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya ba jami’an tsaron da ke kare shi umarnin cewa duk wanda ya kara tare hanya, ya hana jerin gwanon motocin sa wucewa, to a bindige shi kawai.

Umahi ya ce ko kashe mutum aka yi, babu wani abin da zai biyo baya, domin doka ta bayar da wannan iznin.

Ya yi wannan bayani ne ranar Asabar, bayan ya sha da kyar, lokacin da wasu gungun masu jerin-gwanon makoki suka datse titi, suka hana shi wucewa.

Abin ya faru ne a hanyar Onicha, cikin Karamar Hukumar Onicha, bayan ya dawo daga garin su, Uburu Ojaozare, ranar Juma’a wajen karfe 12 na dare.

Ya sanar da cewa wadanda suka tare hanyar sun yi ta gugumara da jami’an tsaron sa, wasu suka fizge bindigar wani soja.

A kan haka ne ya ce ya bada umarni duk wadanda suka tare hanyar to a kamo su a hukunta su. Kuma ya ce sai sun yi Zaman kurkuku.

“Da wani matafiyi suka tare haka, ai fashi za su yi masa. To ni kai na gwamna ban sha da dadi ba, domin sun kwace bindigar soja.

Ya kuma bada umarnin cewa duk masu shirya jerin-gwanon makoki, kada su kara wuce karfe 10 na dare.

Share.

game da Author