Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana cewa a duk shekara sai ta kwashi ‘ya’yanta kaf sun garzaya hutu kasashen waje.
Aisha ta tabbatar da haka ne a yayin da take amsa tambayoyin manema labarai a filin jirgin saman Abuja bayan ta sauka a filin.
” Yanzu kusan shekara 27 kenan ni da ‘ya’ya na duk shekara sai mun tafi yawon shakatawa da hutu a kasashen turai.
Aisha ta ce tana Ji da ‘ya’yan ta matuka wadda a dalilin haka take kebe wani lokaci a duk shekara domin fita kasashen waje da su domin su huta.
Baya ga haka uwargidan shugaba Buhari ta kara da cewa lallai fa a tsakaninta da ‘yan uwan mijinta ba a ga maciji.
Aisha ta tabbatar da cewa ita ce a wani bidiyo da ya karade shafunan soshiyal midiya inda aka nuna ta tana hargowa a wani daki.
Ta bayyana cewa daya daga cikin ‘ya’yan Mamman Daura, mai suna Fatima ta rika daukar wannan bidiyo a lokacin da take wannan balli.
Sai dai kuma ita ma Fatiman ta ce tayi haka ne domin ta nuna wa iyayenta irin yadda Aisha ta ci mutuncin su a wannan gida a lokacin da ta shigo basu nan.
Fatima ta shaida wa BBC Hausa a hira da tayi da jaridar cewa Aisha Buhari ta rika yin kutubol da wasu kay a wannan gida a lokacin da ta far musu babu sallama.