Duk Makircin Ku, Da Yada Karyar Ku, Allah Zai Kare Mutuncin Mai Martaba Sarkisian, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Ya ku ‘yan uwa masu albarka! Kamar yadda kuka ji ko kuka gani, tun jiya asabar 12/10/2019 zuwa yau lahadi 13/10/2019, muka wayi gari da wani makirci da sharri da makiya masarautar Kano mai daraja da albarka suke yada wa, ba domin komai ba sai don kokarin da suke yi wurin ganin sun tabbatar da alwashin da suka daukar wa kawunansu na sharri, cewa sai sun ga bayan wannan masarauta mai daraja, kuma sai sun tarwatsa duk wani abu da magabata masu daraja suka gina, kuma suka bar wa zuri’ar su domin ci gaba da tafiyar da wannan masarauta mai albarka bisa tsarin da ya dace, wanda da yardar Allah, da ikon sa, da karfin sa, ba zasu taba cin nasara akan wannan danyen aiki da mummunan nufi nasu ba!

An wayi gari suna ta yada wata karya, ba don komai ba, sai don kokarin gyara miyar gidan su. Domin kamar yadda kowa ya sani ne, su wadannan miyagun mutane, suna rayuwa ne kuma suna cin abinci da wannan fitina da ke faruwa, tsakanin masarautar Kano mai albarka da gwamnatin Jihar Kano. Domin duk wani mai lura da al’amurra, yasan da cewa wadannan mutane basa so wannan fitana da kare, shi yasa za ka ga cewa sai abu ya lafa, sai su kunno wata wutar sharri domin gwamnati ta sakar masu kudi, su ci gaba da cin karen su babu babbaka.

Kawai sai muka ga wadannan shedanun mutane, mara sa kaunar zaman lafiya, suna yada wata karya a kafafen yada labarai na zamani kamar Facebook, Twitter, WhatsApp, Instagram da sauran su, cewa wai Mai Martaba Sarki ya kori Maja Sirdin Sarki daga mukamin sa. Ga dai kadan daga cikin abin da suke yadawa, na hakaito maku, ba tare da canza rubutun su ba:

“Shin Anya Sarkin cikin gari Dagaske yake son shirin su da gwamna ko kuma akwai wata makarkashiyya? Alhaji Auwalu Maja siddin Sarkin Kano. A yau an sauke shi daga mukaminsa tareda korarsa da kuma iyalinsa daga cikin gidan Sarautar cikin garin Kano. Laifinsa kawai shine ya taryi Gwamna tareda bashi hoton Marigayi mai Martaba Sarki Alhaji Ado Bayero lokacin da Gwamnan yazo wuce wa ta kofar gidan Sarautar cikin garin.”

To yanzu don Allah, ya ku jama’ah, in ban da karya, da kokarin yada sharri, a ina ne aka yi wannan? Sannan yaushe wannan abu ya faru? Sannan wai shin me yasa mutane basa tsoron Allah ne a cikin al’amurran su? Kuma me yasa mutane suka manta da cewa akwai mutuwa da hisabi ne? Kawai ku kirkiri karya da sharri ku yada don cimma wani buri da kuma kokarin faranta wa iyayen gidan ku rai?

Sannan wai shin ma waye Sarkin cikin gari? Sannan don Allah wace Sarauta ce Sarautar Sarkin cikin gari? Sannan yaushe ne aka kirkire ta? Sannan don Allah Kanawa da duk masana tarihin Masarautar Kano, wace Sarauta ce wannan? Shin akwai wata Sarauta mai wannan suna da jahilai suke yadawa?

Ni dai na san wallahi, babu wata Sarauta a Kano sai daya, kuma wannan Sarauta, ita ce kadai duniya ta sani kuma ta yarda da ita, sannan duk wani mai ilimi ita ya sani, wato ta Salihin Sarki, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II. Saboda haka ya ku jahilai, wawaye, makirai, ku sani, wallahi kun yi latti. Da ikon Allah, Allah zai ci gaba da kare mutuncin masu mutunci a duk inda suke. Kuma da ikon Allah, a duk lokacin da kuka kulla wani sharri ko makirci, to sai Allah ya tona asirin ku, domin duniya ta san da cewa ku makaryata ne.

Kuma game da sauran jama’ah, don Allah, ina rokon ku, a duk lokacin da kuka ga irin wannan sharri ana yada wa, ku sani abu na farko, Allah Madaukakin Sarki ya umurce mu da muyi bincike domin gano gaskiyar lamari. Domin a yau, miyagun mutane suna nan, basu da aiki sai yada karya a soshiyal midiya, don cin mutuncin bayin Allah masu mutunci da daraja.

Sannan kuma ku sani, kamar yadda har kullum muke ta kokarin sanar da ku, akwai wasu mutane, suna nan cikin mu, sun hada kai da makiya Musulunci da Musulmai, makiya arewa da ‘yan arewa, domin kokarin ganin bayan mu. Don haka ina kira da mu zama a fadake ko yaushe. Kar mu taba yarda da duk wani da baya son zaman lafiyar arewa da hadin kan ta!

Mu ta banagaren mu, da iya binciken mu, tsakani da Allah, wannan labarin karya da aka yada na sharri, wai Masarautar Kano ta kori Maja Sirdin Sarkin Kano bisa wani abu da ya faru, wannan labari karya ne, masu yada wannan magana suna yi ne don su haifar da husuma tsakanin al’ummah, kuma domin biyan wata bukata ta kan su da ta iyayen gidan su. Da ma tuni Alkur’ani ya fada muna cewa, masu irin wannan dabi’a fasikai ne, wadanda basu bukatar ci gaban al’ummah.

Don haka muna tabbatarwa da al’ummah, musamman ‘yan Jihar Kano, cewa Maja Sirdin Sarkin Kano yana nan daram akan matsayinsa na Maja Sirdi.

Sannan daga karshe, ina mai addu’a, Allah ya taimaki Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Allah ya kara masa imani, lafiya da nisan kwana. Sannan duk masu kirkirar karya da sharri, da masu kulle-kullen makirci, da masu son kawo rashin zaman lafiya a Kano da arewa, saboda cimma wata mummunar manufa ta su, ya Allah, ka tattara dukkan masifar rashin zaman lafiyar ka kai ta har cikin gidajensu da dakunan su, amin ya Allah.

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta wannan sako, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za ku same shi ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.

Share.

game da Author