Kodinatan kungiyar ‘Community Health and Research Initiative’ Aminu Magashi ya bayyana rashin jin dadin sa kan yadda gwamnati ta yi watsi da wadata kasa da isassun motocin daukar marasa lafiya a kasarnan.
Magashi ya bayyana haka na a hira da yayi da jaridar PREMIUM TIMES.
Ya ce idan ba a manta ba a ranar biyar ga watan Faburairu ne gwamnatin tarayya ta kafa fannin kula da marasa lafiya na gaggawa domin inganta aiyukkan fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Mutanen da suka yi hadarin mota, tsofaffi, mata masu ciki, yara kanana na daga cikin mutane da wadannan motoci za ta rika dauka idan wani abu na gaggawa ya taso.
Motocin za su rika bin manya-manyan titunan Abuja zuwa Lokoja, Legas zuwa Ibadan, Doka zuwa Kaduna, Onitsha zuwa Akwa, Legas zuwa Ore da Abeokuta zuwa Legas domin daukan mutane sannan za a siyo su ne daga cikin kason kudaden inganta kiwon lafiya da gwamnati ta ware wato BHCPF.
” Sai dai kuma tun bayan fadin haka da gwamnati ta yi shiru kake ji, ba a sake cewa komai ba ballantana a ce wai an kawo motocin sun fara aiki.
Magashi yace samar da wadannan motoci zai taimaka matuka wajen ceto rayukan mutane da dama da ake rasawa a dalilin hadarin mota a manyan titunan kasarnan.
“A yanzu haka akori kura da motocin mutane ake amfani da su idan ana bukatar gaggauta kai mutum asibiti kida anyi hadari a manyan titunan kasarnan.
“Gwamnati ta saki wadannan kudade domin inganta fannin kiwon lafiya sannan akwai wasu matakai da aka tsara domin ganin an samar da wadannan motoci amma har yanzu ba a ce komai ba.
Bayan haka babban sakataren ma’aikatan kiwon lafiya Abdulaziz Mashi ya bayyana cewa ma’aikatar na yin kokarin gaske wajen ganin an samar da wadannan motoci a kasar nan.
Mashi yace ma’aikatar zata tabbatar cewa kason inganta aiyukkan sashen ba da kula na gaggawa ya kai ga asusun wannan sashe ba tare da an samu wani matsala ba.