Dalilin da yasa gwamnatin Barno ke rusa gidajen karuwai da gidajen giya – Kaka-Shehu

0

Kwamishinan Shari’a na jihar Barno Kaka Shehu Lawn ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta bi gidajen karuwai, Wasu Otel-Otel da gidajen Giya a jihar ta na rusawa shine ganin yadda wadannan wurare suka zama maboyar marasa gaskiya da matattarar ‘yan iska.

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta taba rusa ire-iren wadannan gidaje da Otel-Otel da ake tafka ashararanci a babban birnin jihar, Maiduguri a shekarar 2018.

Lawal yace bayan Gwamnati ta gudanar da bincike akan wadannan wurare ta gano cewa bayan ashararanci da ake tafkawa a wadannan wurare, sun rikida sun zama maboyan ‘yan iskan gari da marasa gaskiya.

” A Wasu wuraren ma mun gano Otel din ya ya koma inda matsafa me kulle-kullen su. A wasu Kuma, za ka ga an tara ‘yan mata ne kanana ana lalata dasu.

” A Otel din Lake Chad dake Maiduguri kuwa abin da muka gano ya kazanta. Kiri-kiri da rana tsaka za ka ga ‘yan mata kanana da basu wuce shekaru 15 suna Zina da Maza, Wasu Kuma suna madigo da juna. A wannan Otel din ba mata kanana ba har matan aure mun Kama suma suna garzayowa wannan Otel din da wasu mazan suna tafka ashararanci.

Lawan ya Kara da cewa baya ga haka, wannan Otel din ya zama dandalin mashaya barasa, muggan kwayoyi da shaye-shayen wiwi sannan kuma matattara ne na maza ‘yan luwadi da mata masu yin madigo.

Daga nan sai ya tunatar da mutane cewa dama can akwai dokar hana haka dake aiki a jihar da ya ba Gwamnati damar rufe irin wadannan wurare da kuma Kama irin wadannan mutane.

A karshen Kaka-Shehu ya gargadi mutane cewa Gwamnati ba za ta nade hannu ta bari wani ko wasu su rika aikata ashararanci a jihar ba a taka musu birki ba.

Share.

game da Author