Shugaba Muhammadu Buhari zai zarce kasar Ingila, domin ziyara ta kan sa, bayan kammala taron kwanaki uku a kasar Saudiyya.
Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ya sa wa hannu, ta ce Buhari zai bar Najeriya yau Litinin, kenan ba zai dawo ba sai bayan kwanaki 21.
Zai bar Saudi Arebiya ranar 31 Ga Oktoba, zai dawo Najeriya a ranar 17 Nuwamba.
Wannan tafiya da zai yi dai ba a ce ga takamaimen abin da zai yi a London ba.
Tsarabar da Buhari zai kawo wa ‘yan Najeriya daga Saudiyya
Taron Saudiyya
A yau Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari zai sake jan zugar tawagar jami’an gwamnatin sa zuwa kasar Saudi Arebiya domin halartar wani taro.
Wannan ne karo na uku da Buhari zai kai ziyara Saudiyya a cikin watannin kadan. Idan ba a manta ba, Buhari ya je Umrah a cikin watan Mayu kafin a sake rantsar da shi a karo na biyu.
Kwana daya bayan sake rantsar da shi kuma, wato mako guda bayan dawowar sa daga Umra, sai ya sake lulawa kasar Saudiyya, inda ya halarci wani taro da ya shafi tattalin arziki.
Tafiyar da Buhari zai yi yau Litinin, zai halarci wani taro ne na kasashe 90 a kan Bunkasa Tattalin Arziki Da Karfafa Zuba Jari.
Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ne ya dauki nauyin shirya taron, wanda wakilai sama da 4,000 za su halarta.
A wannan ziyara, Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa za a yi kwanaki uku, wato daga 29 zuwa 31 Ga Oktoba ana gudanar da taron.
JIRAN TSAMMANIN TSARABA DAGA SAUDIYYA
Fadar ta Shugaba Buhari ta bayyana cewa Buhari zai gana da manyan masana’antu, inda zai nuna masu alfanun da ke tattare da su matukar suka garzayo cikin Najeriya domin su zuba jarin su.
Sannan kuma Buhari zai gana da Shugabannin Kamfanin Fetur da Gas na Saudi Aramco, domin ya shigo Najeriya ya samu damar gagarimin aikin farfado da matatun mai na Najeriya.
Akwai kuma gagarimar farauta da Buhari zai yi a zauren taron, inda ake sa ran zai samu kamfanonin da za su yi aikin shimfida bututun gas na tsawon kilomita 614.
Wannan bututun gas kamar yadda Fadar Shugaban Kasa ta bayyana, za a yi aikin shimfida shi ne tun daga Ajaokuta ya bi ta Kaduna har zuwa Kano.
Sannan kuma sanarwar ta nuna cewa a yanzu masu zuba jari daga kasashen duniya sai kwararowa cikin Najeriya suke yi, ganin cewa a yanzu dama ta samu, yanayin kasuwanci mai tsabta ya wanzu a kasar, tun bayan da Buhari ya kafa mulki.
“Daga tsakiyar shekarar 2018 an samu karin dala biyan 12 daga masu zuba jari a Najeriya. Amma ya zuwa tsakiyar 2019 har wannan jarin da aka shigo aka zuba ya kai dala bilyan 14.” Inji Fadar Shugaban Kasa.
Cikin tawagar da za su raka Buhari, akwai Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi, Aminu Masari na Katsina, Babagana Zulum na Barno.
Akwai kuma Karamin Ministan Harkokin Waje, Zubair Dada, Ministan Cinikayya da Masana’antu, Niyi Adebayo, Karamin Ministan Fetur, Timiprie Sylva, Ministan Sadarwa, Isa Pantami, Mashawarcin Buhari a fannin tsaro, Babagana Monguno da sauran su.
Za a yi taron a Riyad, babban birnin Saudi Arebiya.
Discussion about this post