Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa bashi da wani wanda ya fi mishi tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan a rayuwar sa.
“ Tsohon shugaban kasa ba shugaba na bane kawai kusa ni, malamina ne kuma abin koyi na ne. Ina so kusa ni cewa bayan Allah da nake bautawa to sai Shugaba Jonathan. Ku sani ba zan yarda a yi wani abu da zai kunyata ko kuma ya kaskantar da tsohon shugaban kasa Jonathan ba. Ina son kowa ya san haka.
Gwamna Bala ya ce shi da kansa tsohon shugaban kasa Jonathan ya umarci shi da ya shiga tsakanin rikita rikitan da ke neman ya tarwatsa jam’iyyar PDP a jiha Bayelsa domin kawo karshen haka.
“ Bayan jam’iyyar ta nada ni, shima tsohon shugaban mu ya umarce ni da in shiga cikin wannan Magana. A dalilin haka kuwa a ganina komai ya kusa wanyewa ke nan.
Gwamna Bala ya kara da cewa babu abinda zai sa yayi wa Jonathan yankan baya a siyasa ko a rayuwa kuma duk wanda yace zai yi masa haka za su sa kafar wando daya dashi musamman game da wannan zabe dake tafe a jihar.
“ Ban taba neman abu a wurinsa yace a’a ba. Shine shugaba daya da baya duba yankin da ka fito idan zai yi maka wani abu. Ya nada ni ministan Abuja ba tare da na fito daga yankin sa ba. Ba zai taba amincewa ace bayan tashi-fadin da yayi wajen ganin jihar Bayelsa ta ginu gadagau a siyasance ba kuma yanzu sai ace wai za a ruguza wannan gini da aka wahala ana yi ba.
A karshe yace za su koma su zauna su natsu domin tsara yadda jam’iyyar za ta yi nasara a zabe mai zuwa.