Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira da a rika wayar da kan mutane game da cutar daji cewa yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.
Aisha ta fadi haka ne a taron wayar da kan mutane game da cutar wanda gidauniyar ‘Medicaid Cancer’ ta shirya.
Ta ce kamata ya yi Najeriya ta yi koyi da matakan kawar da wannan cuta da wasu kasashen Afrika suka yi.
“ A yanzu haka wasu kasashen Afrika na yi wa mutane musamman mata allurar rigakafin cutar da ya kamata ace mu bi wannan sahu a kasar nan.”
Bayan haka uwar gidan gwamnan jihar Kebbi kuma shugabar kungiyar ‘Medicaid Cancer’ Zainab Bagudu ta yi kira ga sauran sassan gwamnati da su hada hannu da gwamnati tarayya domin samar da kula na gari wa masu fama da cutar.
Zainab ta ce kamata ya yi gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su taimaka wajen samar da na’urorin gwajin cutar da rage farashin magunguna domin tallafa wa rayuwar masu dauke da cutar a kasar nan.
Daga nan shugaban kungiya mai zaman kanta ‘Monitor Health Care’ Femi Ogunremi ya yi kira ga gwamnati kan wayar da mata game da cutar dajin dake kama nono da mahaifar mace cewa mata da dama na kamuwa da cututtukan a kasar nan.
Idan ba a manta ba a watan Faburairu ne kungiya mai zaman kanta ‘Project Pink Blue’ ta yi wa mutane gwajin cutar daji kyauta a Abuja.
Kungiyar ta yi haka ne domin wayar da kan mutane game da cutar ganin cewa masu dauke da wannan cutar a Najeriya na mutuwa saboda rashin samun kula.
Project Pink Blue ta yi kira ga mutane da su rika kula da irin abincin da suke ci tare da yawan motsa jiki cewa rashin haka na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar.