CETO DALIBAN CHIBOK: Goodluck Jonathan ya karyata Tsohon Shugaban Ingila

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya kira tsohon shuhaban kasar Birtaniya makaryaci, bayan ya zargi Jonathan da kin amincewa su ceto daliban Chibok.

James Cameroon ya fada a cikin wani littafin sa cewa ya kira Jonathan ya shaida masa cewa jami’an tsaron Ingila sun gano inda aka kai daliban Chibok, amma ya ki bada iznin su shigo su ceto su.

An dai sace daliban ne sama da 200 tun a ranar 14 Ga Afrilu, 2014.

Jonathan ya yi sauri ya karyata zargin da James Cameron ya yi a littafin mai suna “For the Record.”

A cikin martanin Jonathan, akwai ya rubuta wa Cameron din da Barrack Obama da shugaban Faransa na lokacin, har ma da shugaban Isra’ila cewa su taimaka a gano inda daliban Chibok su ke.

“Takardu ne a rubuce, kuma a yanzu haka akwai su a Fadar Shugaban Kasa. To ta yaya ni da na rubuta musu takardar neman agaji, zai ce wai na ki yarda a ceto su?”

Daga nan Jonathan a dai cikin martanin wanda ya watsa a shafin sa na Facebook, ya bayyana yadda ya bai wa jami’an tsaron Birtaniya iznin shigowa Najeriya domin su ceto wani Baturen Ingila da na Italiya, wato Chris MacManaman da Franco Lamonimona da Boko Haram suka suka sace a Sokoto.

DON NA KI HALASTA AUREN JINSI A NAJERIYA CAMERON YA TSANE NI
Jonathan ya ce tsohon shugaban Ingila, Cameron ya tsane shi ne, saboda ya ki yarda ya watso bakar aniyar sa ta ruruta auren jinsi a Najeriya.

“Lokacin da James Cameron ya sa wa dokar halasta auren jinsi a Ingila, kowa ya ji lokacin da ya ce zai yi kamfen din watsa halascin auren jinsi a duniya.

“To ya kira ni, ya ce zai turo min jami’an da za su tsara daftarin dokar halascin nan a Najeriya. Da suka zo na ce hakan ba zai yiwu ba.

“Daga nan sai ya fara tsana ta. Ya rika damu na da magiya cewa a amimce a rika yin auren jinsi a Najeriya. Yayin da ma ya ga na sa hannu a kan haramta auren jinsi a Najeriya, sai ya fi nuna min tsana karara.”

ZARGIN SIYASA A NADIN SHUGABANNIN TSARO
Jonathan nan ma ya ce karya Cameroon ke masa, domin sau biyu ya ma tsige shugabannin tsaro, domin a tabbatar ya na kokari a batun yaki da Boko Haram.

Idan ba a manta ba, wadda ta canji Cameroon, wato Theresa Maya, a ranar 8 Ga Maris, 2017, ta ce karya ne, jami’an tsaron Ingila ba su gano inda daliban Chibok su ke ba.

Share.

game da Author