Buhari zai fara ladabtar da hukumar da ta kasa tabuka tara haraji

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta sa ido sosai a kan yadda hukumomin tara kudaden haraji ke tara kudaden shiga.

Da ya ke jawabi a yau Talata ga daukakin ‘yan Najeriya, a zagayowar Ranar ‘Yanci, Buhari ya ce kudaden shiga abu ne mai muhimmanci ga ci gaban kasa. Don haka baya ga sa-ido, gwamnatin sa za ta fara daukar kwakkwaran mataki ga duk hukumar da ta kasa tara kudaden harajin da ta yi hasashen tarawa a cikin kasafin kudin ta.

Sai dai kuma ya ce za a rika bayar da goron tukuici ga duk hukumar da ta yi wata bajintar tara kudaden shiga masu yawa.

Ya kara da cewa gwamnatocin baya sun ki maida hankali wajen inganta hanyoyin samun kudaden shiga da ba na man ferur da gas ba. Wadannan hanyoyi kuwa inji Buhari, su na samar da kashi 40 bisa 100 arzikin kasa.

Hanyoyin da Buhari ya ce gwamnatocin baya sun yi watsi da su, sun hada: Noma, kiwo, nishadantarwa, ma’adinai, gina masana’antun da za su samar da milyoyin ayyuka ga dimbin matasa da sauran su.

Sai kuma ya yi tutiya da karuwar da kudaden asusun waje da Najeriya ke tutiya da su, wadanda Buhari ya ce yanzu sun kai Dala bilyan 42.5, sabanin Dala bilyan 23 a cikin 2016.

Share.

game da Author