Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi zuwa kasar Saudiya Arabiya ranar Litinin.
Buhari zai halarci taron bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya da saka jari ne da za ayi a kasar Saudiyya.
Idan ba a manta ba a karshen wannan mako ne shugaba Buhari ya dawo daga kasar Rasha wajen halartar taro irin haka na na yin nazari da bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika.
A tawagar da zasu raka Buhari kasar Saudiyya akwai gwamnan jihar Barno Babagana Zulum, Aminu Masari na Katsina da Abubakar Bagudu na jihar Kebbi.
Baya ga wadannan gwamnoni akwai ministocin Mai, Ciniki da masana’antu, Sadarwa, da ministan harkokin waje.
Mai ba shugaban kasa shawara a harkokin tsaro Babagana Mongonu da shugaban hukumar SSS, Ahmed Abubakar.
Bayan taron da za ayi kwana uku ana yi, Buhari zai yi Umrah kafin ya dawo kasa Najeriya.