Buhari ya yi wa Minista Akpabio gudummawar gobarar Titi

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sanarwar dauke Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NNDC) daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), zuwa Ma’aikatar Raya Harkokin Neja Delta.

Wannan ma’aikata dai tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ne ministan ta. Kuma ta na daga cikin ma’aikatar da ake narka wa kudaden gudanar da ayyuka.

Ayyukan ma’aikatar shi ne inganta kayayyakin rayuwar mazauna yankin Neja Delta.

Idan za a iya tunawa, Akpabio ya fice daga PDP, ya koma APC cikin 2019 kafin zabe. Za tsaya takarar sanata, amma bai yi nasara ba. Buhari ya nada shi Ministan Raya Yankin Neja Delta.

Wannan ma’aikata ta NNDC da aka maida a karkashin Minista Akpabio, ita wuri ne da gwamnati ke narka makudan kudade domin kula da yankin Neja Delta, musamman gudanar da ayyuka inda ayyukan hako danyen man fetur ya gurbata wa muhalli.

A cikin jawabin na Buhari, ya kara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da inganta hanyoyin samun kudaden shiga ta danyen man ferur, tare da ririta abin da ake samu sosai. Sannan kuma gwamnati za ta fadada wasu hanyoyin samun kudaden shiga wadanda ba na ganin danyen man fetur ba.

Share.

game da Author