A kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sun daina kashe kudade barkatai, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da wani sabon tsarin rage kashe kudade da aka shigo da shi.
Tsarin zai rage yawan fitar ministoci da sauran manyan ma’aikatan gwamnati da shugabannin hukumomi zuwa kasashen waje, da nufin kara ririta kudaden shigar da gwamnati ke samu, ana aiki da su a inda ya dace.
Kamar yadda wata sanarwa daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta nuna, dukkan Ministoci, Shugabannin Hukumomin Gwamnati da suran manyan jami’ai, su rika aika wa ofishin Sakataren Gwamnatin dukkan bukatun su na tafiye-tafiye kasashen waje domin a duba yiwuwar mai yiwuwa.
Ana so su rika aikawa da wuri, kafin akarshen watanni uku na farkon shekara.
Kuma za su rika yin bayanin muhimmancin wannan tafiye-tafiye idan ma har an amince da yin tafiyar din.
Sannan kuma sanarwar ta kara da ce duk wanda aka amincewa ya yi wata tafiya ko a nan cikin kasa ko a kasar waje, wadda gwamnati za ta dauki nauyin sa, to zai kasance lallai sai tafiya wadda wani aikin gwamnati ne ai kai shi, kuma sai ya gabatar da kwakkwarar shaida.
Sanarwar ta ce ba za a bada iznin yin kowace tafiya ba, sai fa wadda ake ga gamsasshiyar hujja da shaidar cewa tafiya ce wadda kasa za ta amfana sosai da sosai.
“A duk lokacin da wani minista zai fita kasar waje, idan har fitar ta kama, to kada ‘yan rakiyar sa su wuce mutane hudu, wadanda daga cikin su zai kasance akwai Daraktan bangaren da ke da alhakin aikin da tafiyar ta kunsa, Jami’in Tsare-tsare da kuma hadimin ministan guda daya tal.
“Duk wata tawagar da ba ta kai mukamin tawagar minista ba, to idan har tafiya waje ta kama, kada ta wuce ta mutane uku.
Shugaba Buhari ya amince ministoci da manyan sakatarori da shugabannin ma’aikatu da sauran su, su rika hawa babbar kujerar jirgin sama (First/Business Class. Amma sauran ‘yan rakiya su rika hawa bangaren kwanyamin sauran fasinjoji, wato ‘Economy Class.’
Sannan kuma za a daina bayar da kudaden guziri idan za a fita kasashen waje. Haka dai sanarwar ta bayyana.
An kuma umarci Babban Akanta Janar na Kasa da ya dauki duk wata bukatar kashe kudaden da ta kauce wa wannan sharudda a matsayin harkallar da ba za a amince wa ba.
Discussion about this post