BOKO HARAM: Gwamnatin Barno za ta dauki ‘yan tauri 10,000

0

Gwamnatin Jihar Barno ta fara daukar hatsabiban ‘yan tauri, mafarauta, masu layar zana, ki-bugu, shashatau da sauran masu asiran kulumboton gargajiya domin magance Boko Haram.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an fara daurar da nufin daukar mutane 10,000, amma a asirce.

“To amma ka san abin da duk aka ce za a dauki dubban jama’a aiki, ba zai boyu ba.” Inji majiyar da ba ta so a bayyana sunan ta.

PREMIUM TIMES ta lura da yadda wasu bakin-ido ke ta kwarara cikin birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Barno. Wadanda ke kwarara cikin garin, suka damfare ne a cikin motoci, daga mai bindiga sai masu takubba, gariyo, layu. Wasu sun yi jigida da guraye, wasu da daure da kambuna da karhuna.

“Gwamnatin Barno kamar ta fara nuna gajiya da yadda yaki da Boko Haram ya ki ci, ya ki cinyewa, sama da shekaru goma. Shi ya sa ta fito da gagarimin shirin daukar ‘yan tauri domin su ma su taimaka.

“Tuni har kamar ‘yan tauri 2000 sun shigo Maiduguri. Kuma sojoji ne ke tantance su, sannan a dauke au aiki.” Haka majiya ta tabbatar wa wakilin mu.

An dai yi gagarimar gayyatar ‘yan taurin ne daga Jihohin Arewacin kasar nan da makwabtan kasashe, ciki har da Jamhuriyar Nijar.

Idan ba a manta ba, cikin watan Janairu, gwamnatin Barno ta dauki maharba 500 aikin taimakawa a murkushe Boko Haram.

Cikin makonmi biyu da suka gabata kuma, Gwamna Zulum ya je Makka, ya dauki hayar malamai 30 domin su rika yin addu’o’i d dawafi a Ka’aba, neman Allah ya kawo karshen fitinar Boko Haram.

Share.

game da Author