BOKO HARAM: Gwamnati zata saka yara miliyan 10.2 makarantan Boko

0

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta kashe akalla Naira biliyan 10 domin saka yara miliyan 10.2 a makarantan boko a fadin kasar nan.

Wadannan adadin yawan yara sune aka kididdiga ke gararramba a titunan kasar nan ba tare da suna zuwa makarantan Boko ba.

Ministan ilimi Adamu Adamu ya sanar da haka a taron gabatar da tsare-tsaren da ma’aikatar Ilimi ta shirya domin inganta fannin ilimi a kasar nan da aka yi a Abuja.

Adamu ya ce gwamnati za ta dauki tsawon shekaru biyar tana aikin saka wadannan yara a makarantun boko a kasarnan.

“Duk shekara gwamnati na sa ran zata saka akalla yara miliyan biyu daga cikin adadin yawan wadannan yara a makarantun boko. Za mu yi wannan aiki ne tare da hadin guiwar gwamnatocin jihohi.

Bisa ga shirin duk shekara gwamnatocin jihohi za su ware wani kaso wanda za a hada da kason da gwamnatin tarayya ta ware domin ganin komaai ya zo cikin sauki.

Adamu ya kara da cewa gwamnati za ta hada hannu da malaman addini, sarakuna domin wayar da kan mutane musamman mazauna karkara sanin mahimmancin saka ‘ya’yan su a makarantun boko.

“Gwamnati zata rage kudin makaranta domin ‘ya’yan talakawa su samu su iya shiga faven domin a fafata dasu.

Idan ba a manta ba bincike ya nuna cewa akalla yara miliyan 10.2 na gararramba a titunan kasar nan ba tare da sun samu ilimin boko ba.

Binciken ya kuma nuna cewa kashi 60 bisa 100 daga cikin su ‘ya’ya mata ne da a ciki akwai wadanda suka fara makarantar amma suka watsar da wadanda basu shiga makaranta ba ma kwata-kwata.

Share.

game da Author