BOKO HARAM: Abin da ya sa mu ka nemi hadawa da addu’a – Buratai

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa sojoji sun nemi hadawa da addu’o’i wajen yaki da Boko Haram ne domin a dakile yadda Boko Haram din ke yin farfaganda.

Buratai, wanda Burgediya Janar Timothy Olowomeye ya wakilta a wurin taron horas da Limaman Kiristoci a Sokoto, ya ce “mun nemi hadawa da wa’azi da addu’o’i wajen yaki da Boko Haram da ma sauran tashe-tashen hankula.

“Yin amfani da makami kadai da sojoji ba zai iya kakkabe Boko Haram ba.

“Idan aka samu wata kwakkwarar hanyar da a yaye musu mummunar akidar da ake cusa musu, zai yi tasiri sosai a kan su da kan mummunar akidar rikau mai zafi da aka cusa musu a kwakwalwar su.

Buratai ya ce Najeriya da sauran kasashen duniya da dama sun dade su na fama da rikice-rikicen da ke da nasaba da addini, tattalin arziki da wadanda ke da dalilai na siyasa.

“Wadannan tarzoma kuwa sun haddasa asarar rayuka, dukiyoyi, sannan kuma kowa ya maida hankali wajen neman sauki daga bangaren gwamnati.

“Shugaba Muhammadu Buhari na ci gaba da kawo sauki da mafitar magance rigingimun da suka addabi kasar nan wajen kara wa sojojin Najeriya kwarin gwiwa matuka. Ba ma a bangaren sojoji kadai ba, har a bangaren sauran jami’an tsaro.

Ya ci gaba da cewa imanin da ‘yan Boko Haram suka shi ne har yau ya zama dole a rika hadawa da bangaren addini aka warware mummunan tunanin da ake cusa wa matasa a kwakwalwar su.

Ya yi fatan taron zai inganta dukkan hanyoyin da za a bi wajen wanke kwakwalwar wadanda ake cusa wa mummunar akidu na addini.

Sama da shekara kusan goma kenan ana ta fama da Boko Haram, amma an kasa murkushe su.

Su na kara samun kwarin gwuiwa ne ta hanyar akidar da ake dasa musu a zukata, ta hanyar yin amfani da tashin hankali da kisan jama’a da sunan jihadi.

Share.

game da Author