BINCIKE: Yadda aka yi watsi da kwangilolin gina gadojin Wase da Mangu bayan an biya sama da naira miliyan 225 a Filato

0

A yankunan karkarar Najeriya, ciki har da Jihar Filato, rashin ingantattun hanyoyi a yankunan karkara kan kawo cikas wajen kokarin samar da wadataccen abinci da kuma samar da ayyukan raya al’umma a cikin yankunan.

Hukumar Samar da Abinci ta Duniya, da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa kashi 80 bisa 100 na abincin da ake nomawa a duniya duk a gonakin mazauna karkara ake samar da shi.

Wannan matsala ta zama abin damuwa matuka ga mazauna yankunan Kananan Hukumomin Mangu, Bokkos da Wase a Jihar Filato. Ga rashin ruwan sha, ga rashin hanyoyin shiga lunguna da yankuna, ga rashin wutar lantarki sannan kuma ga rashin kananan asibitocin kula da mazauna yankunan karakara.

Rashin kyawon hanyar shiga lungunan karkara kan janyo wa talakawa manoma rashin kaiwa ga samun damar karbar tallafin kudade, samun horo da ilmantarwa har ma da kula da lafiyar su.

Wannan ke haddasa fatara da talauci da kuncin rayuwa su yi katutu a yankunan karkara.

Duk wasu ayyuka da ake magana a nan, an gudanar da su ne ta hanyar sa-idon Hukumar Raya Kogin Benuwai (LBRBDA), a karkashin Ma’aikatar Samar Da Ruwan Sha ta Kasa.

KAUYEN KADIM

Sai da wakilin PREMIUM TIMES ya shafe awa uku da minti 40 cur kafin ya gano kauyen Kadim daga garin Bokkos, inda aka bayar da kwangilar naira milyan 400, wadda aka bayar ta tsawon shekaru uku.

Aikin hanya ne da ya fara daga Horop, ya bi ta Kaban ya zarce Kadim. Da farko tsohon Sanata Joshua Dariye ne ya nemi a bayar da aikin cikin 2016, akan kudi naira milyan 120.

Aiki na gina titin kwalta mai tsawon kilomita 20, da kwalbatoci da gadoji a Bokkos, da ke Shiyyar Sanatan Filato ta Tsakiya.

Aikin ya biyo ta kauyen Horop, mahaifar Dariye, inda a can aikin kwalta ya kai har can.

Cikin 2017 kuma sai Dariye ya sake neman gwamnatin tarayya ta sake yin wannan aiki a kan kudi naira milyan 100,000,000.00

Har ila yau an sake saka aikin cikin kasafin 2018, akan kudi naira milyan 200,000,000.00

Kafin a fara karce hanya a fara aikin cikin 2019, mazauna kauyen Kadim, tunda ba su da asibiti, sai dai su dauki marasa lafiya zuwa Horop, mai nisan kilomita 15.

Rabon mutanen kauyen da shan ruwan burtsatse tun cikin 2014, lokacin da burtsaren su ta kafe karkaf.

Mai kula da aikin hanyar, Sunday Ngolot, ya ce aikinn hanyar ya tashi daga Kadilam, amma ya tsaya a Kadim. Iyakar nan aka amince a yi aikin ya zuwa yanzu.

Wani kawun Dariye mai suna Ngolot, ya shaida wa wakilinmu cewa da yardarm Allah idan gwamnati ta sa hannun amincewa, to za a zuba wa hanyar kwalta.

Ya ce gwamnati ta dai bada umarnin a keta jeji a buda hanya, amma ba a bada aikin zuba mata kwalta ba tukunna.

Wakilin PREMIUM TIMES ya samu kamfanin da ke yin aikin a hanyar, mai suna Tilley Gyado and Co.

Amma Ngolot, ya ce injiniyan hanyar, wanda kanin Dariye ne mai suna Daniel Dariye, ba ya nan, ya shiga gari. “Amma kudin da kawai aka sakar musu shi ne na karce kasa da jeji domin a gyra hanyar burji, banda na shimfida kwalta tukunna.”

Makonni hudu wakilin Premium Times na kokarin ganin Daniel, amma sai bai yi katari da shi ba. An ce masa ya na asibitin Gwagwalada, inda yayan sa Joshua Dariye ke kwance asibisiti.

Joshua Dariye a halin yanzu ya na fuskantar daurin shekaru 14 a kurkukun Kuje.

Dariye ya yi gwamnan Filato daga 1999 zuwa 2007.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Daniel Dariye, ya ce bai san komai ba game da aikin kwangilar gina titin.

Ya ce shi kula da aiki ne kawai na sa. Sai dai kuma ya aika da lambar wakilinmu da Joshua Dariye, wanda nan da nan ya kira wakilin na mu.

DARIYE YA KARE KAN SA

Dariye ya shaida wa wakilin mu cewa magana a kan aikin kwangilar ba za ta kammala ba, har sai wakilin na mu ya je gidan kurkukun Kuje ya same shi.

“Bari na fada miki, ni ma fa na yi aikin jarida a baya. Wannan binciken ba PREMIUM TIMES ba ce ta bijiro da shi. Daukar nauyin ta aka yi domin ta yi binciken. Ai ni ba yaro ba ne, na girme ki.” Haka Joshua Dariye ya shaida wa wakiliyar mu ta wayar tarho.

Dariye ya ce an zarge shi da karkatar da kukaden aikin, amma kuma a gaskiya, inji shi, kudaden aljihun sa ya iyar aikin da aka ga an fara.

“Ke bari na yi miki gar-da-gar, akwai aikin dam na Mangu da aka yi watsi da shi kuma akwai aikin titin Panyam zuwa Shendam duk an yi watsi da su. Me ya sa ba a maganar wadannan sai wannan kawai? Ni tunda ma abin haka ne, na shirya a fito a yi fadan. Wanda duk ta tsokane shi zai gane kuren sa, ni ma na shirya.

“Waccan shekarar da wannan shekarar duk gwamnati ba ta saki kudi an ci gaba da aikin ba. Me ya sa ba a maganar aikin da aka watsar na hannun Jonah Jang da Useni, sai na hannu na don kawai ina da matsala da sanatan?

“An kama ni an garkame a kurkukun Kuje, rashin lafiya ta kayar da ni, an garzaya an kai ni asibiti tun cikin Nuwamba na bara. Wannan duk bai ishe su ba, yanzu kuma so suke su kara min wata ukubar da azabar, haba. Wannan dai ba za ta yiwu ba.” Haka ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho.

Banda ta bangaren Dariye akwai sauran wuraren da aka yi watsi da wasu ayyuka sun hada da aikin gadar Kombili zuwa Daika, cikin Karamar Hukumar Mangu.

Su ma ba su da komai na more rayuwa a yanki. Da cocila ko a-c-falfal su ke ganin haske idan dare ya yi. Idan su na bukatar kudin kashewa, sai sun dauko amfanin gonar su sun kai Mararabar Pushit sannan su sayar.

Sannan kuma akwai aikin gadar Kadarko zuwa Wase, wadda ita ma an karbi kudi amma duk an yi watsi da ita.

Share.

game da Author