BINCIKE: Shin Ko matse fitsari, Cin abinci ana kallon talabijin na kawo tabuwar hankali?

0

Bincike ya bayyana cewa a duk shekara mutane akalla 2,710 na kamuwa da matsalolin da kan jirkita kwakwalwa a wannan kasar.

Hakan na aukuwa ne a dalilin hatsari, fama da cututtuka da kan sa a samu matsala a kwakalwa da kan kai ga tabuwar hankali da sauransu.

A dalilin haka wasu likitoci da suka gudanar da bincike sun bayyana wasu dabiu da kan sa fada cikin matsalar tabuwar hankali idan ba an yi taka tsantsan bane.

Wadannan halaye sun hada da cin abinci da safe, samun isasshen barci, rage shan zaki, guje wa yawan yin barci musamman da safe, cin abinci da ake kallon Talabijin ko kuma aiki da Komfuta, sa hula ga maza da kuma dan-kwali ga mata, sa safa idan za kwanta, yawan matse fitsari idan ana ji.

Tun bayan wannan bincike, wasu Likitoci da bam suka dulmiya cikin kogon kimiyya da binciken kwa-kwaf domin gano sahihancin wannan bincike na wadancan likitoci da suka zayyano wadannan halayya.

Sakamakon sabon binciuken Dalla-Dalla

1. Rashin cin abincin safe

Cin abinci da safe musamman ga yara da mata masu ciki abu ne da likitoci ke yawan yin kira akai.

Sun ce cin abinci da safe na taimakawa wajen kaifafa kwakwalwa musamman idan mutum na bukatan yin zurfin tunani.

Sai dai kuma binciken kimiya ya nuna cewa babu alaka da rashin yin haka da dodewar kwakwalwa ko kuma sa a zauce.

Binciken ya nuna cewa kwakwalwar mutum kan yi aiki sosai ne ma idan mutum na yawaita yin azumi ko kuma bai ma ci abincin da safe ba. Bincike ya nuna yi ko rashin yin haka bashi da wani alaka da kwakwalwar mutum.

2. Rashin samun isasshen barci

A nan ma likitocin sun gano cewa dodewar kwakwalwa ko kuma fadawa cikin matsalar samun tabuwar hankali ba shi da nasaba da rashin samun bacci.

Sai dai sunce dama can binciken ya nuna cewa matsalar dake shafan kwakwalwa a dalilin rashin barci matsala ce da aka gano a wasu beraye da aka yi gwaji da su, sannan har yanzu babu tabbacin ko rashin samun isashen barci kan iya kawowa saitin kwakwalwar matsala.

3. Yawan Shan zaki

Tabas bincike ya nuna cewa yawaita shan zaki na cutar da kiwon lafiyar mutum domin a dalilin haka akan kamu da cututtuka kamar ciwon siga, koda, daji, da sauran su.

Amma har yanzu dai babu binciken da ya nuna cewa zaki na cutar da lafiyar kwakwalwar mutum sai dai ma ya kara kaifin ta.

4. Yawan yin barci musamman da safe

Yawaita yin abu na da nashi illar sannan wani bincike ma ya nuna cewa yawan yin barci da safe na da alaka da kamuwa da cututtukan dake kama zuciya, kamuwa da ciwon siga, kiba da rashin yin tunani mai zurfi.

Amma bayan haka babu wani alaka da yawan yin barci da safe yake dashi da cutar da kwakwalwa.

5. Matse ko kuma kin yin fitsari a lokacin da ake jin shi

Wasu likitocin sun ce kin yin fitsari a lokacin da ya kamata na dakushe kwakwalwa sannan yin haka na hadassa cututtuka kamar sanyi da sauran su.

Har yanzu dai bincike bai nuna cewa kin yin fitsari a lokacin da ake ji ba na illata kwakwalwa.

6. Kallon Komfuta ko kuma talabijin a lokacin da ake cin abinci

Yawan yin haka na sa a rika ramewa ne kawai saboda rashin maida hankali wajen cin abinci a natse amma babu alaka da yake dashi da dodewar kwakwalwa.

7. Daura Dankwali ko kuma saka Hula ko saka safan kafa idan za a yi barci

Yin haka na da matukar mahimmanci musamman a lokacin sanyi domin hakan na daga cikin hanyoyin dake hana mutum kamuwa da mura ko kuma cutar hakarkari wato ‘Pneumonia’.

Amma likitocin sun bayyana cewa tabbas bashi da alaka da kwakwalwar mutum ko kuma ko wai yayi sanadin dodewar ta har a samu tabuwar hankali.

Share.

game da Author