Idan ba a manta ba wani likitan yara dake aiki a babban asibiti dake babban birnin jihar Edo, Benin, mai suna Ovo Ogbinaka ya bayyana cewa shan uwan sanyi na cutar da kiwon lafiyar mutum.
Ogbinaka ya bayyana cewa shan ruwan sanyi na haddasa cutar da ke sa a kamu da bugawan zuciya, daji da samun matsala wajen abinci a ciki.
A dalilin wannan rahoto wannan likita ya gargadi mutane da su rage shan ruwan sanyi domin gujewa kamuwa da irin wadannan cututtuka.
Sai dai kuma wasu likitoci dake ‘National Heart, lungs and Blood Institute’ da ‘Nataional Cancer Institute’ dake Kasar Amurka sun musanta gaskiyar wannan bincike na dakta Ogbinaka suna masu cewa duk camfi ne.
Sun ce shan ruwan sanyi baya cutar da kiwon lafiyar mutum ta kowace hanya domin da zaran mutum ya kwankwadi ruwan sanyi a cikin minti biyar runan ke yi sannan ya zama ruwan dumi sannan ya raba kansa zuwa sassan jiki.
Likitocin sun ce ruwan sanyi ba ya sa mutum a kamu da cutar daji, bugawar zuciya ko kuma ya hana abinci markaduwa a cikin mutum ba
“Haka kuma idan mutum ya ci abinci mai sanyi cikin mutum sai ya mai dashi mai zafi domin cikin mutum dumi yake da shi.
Likitocin sun gargadi mutane da su rage yawan shan ruwan sanyi ganin cewa yawaita yin abu na da illa ga ko da ace shan shi daidai-daidai ba shi da matsala.
Discussion about this post