BINCIKE: Hadin kai da kishin kasa ya yi karanci a zukatan ‘yan Najeriya

0

Wani kwakkwaran bincike da cibiyar ‘African Polling Institute’ ta fitar a ranar Talata ya nuna cewa akwai karancin gaskiya, amana, hadin kai da kuma kishin kasa a zukatan ‘yan Najeriya.

Shugaban Cibiyar, Bel Ihua ya bayyana cewa akwai bukatat Gwamnatin Tarayya ta bijiro da hanyoyi da tsarin da zai kara cusa kaunar juna, kishin kasa da kuma nuna goyon bayan gwamnati daga al’ummar kasar nan baki daya.

Shugaban na kungiyar API, ya kara da cewa akwai kuma bukatar a rika aiwatar da ayyukan inganta rayuwar al’umma a ko’ina cikin kasa, yadda kowane bangare zai gamsu da cewa gwamnati ta san da zaman su, kuma ta kula da su.

API ta yi duba da kuwa auna nauyi da gejin kishin ‘yan Najeriya tare da kaunar juna ne ta fuskoki biyar, da suka hada da: Shiyyanci/Bangaranci, Gaskiya, Amana/Amanna, Adalci da kuma Cancanta.

An nemi ra’ayoyin mutane 7, 901, inda kowa ya bayar da na sa ra’ayin. Guda 5, 019 daga cikin su kuwa duk tattaunawa ce aka yi da su gaba-da-gaba, ta hanyar yin tattaki har inda suke a gana da su.

SAKAMAKON BINCIKE

An gudanar da wannan bincike ne daga ranar 24 Ga Afrilu zuwa 20 Ga Mayu, 2019.

Sannan kuma an yi amfani da harshe ko yaruka biyar, da suka hada da Turanci, Hausa, Yarabanci, Igbo da kuma Gargaliyya, wato
Turancin Pidgin.

KISHIN KASA

1 – Kashi 82% sun fi tinkaho da kabilar su, sannan sai tutiya da Najeriya.

2 – Kashi 25% sun fi kishin kabilar su fiye da Najeriya.

3 – Kashi 10% kishin kabila tantagarya ne a zukatan su, babu kishin Najeriya ko kadan.

4 – Kashi 45% sun yi amanna cewa kawunan ‘yan Najeriya ya kara rabuwa sosai, daga shekaru 4 da suka gabata zuwa yau.

5 – Kashi 26% na ganin cewa a yanzu ne ma kawunan ‘yan Najeriya ya fi haduwa.

6 – Kashi 29% kuwa cewa suka yi kishin kasa bai ragu ba, kuma bai karu ba.

ADALCI

1 – Kashi 70% sun yi amanna cewa akwai wasu shafaffu da mai a Najeriya, wadanda doka ko hukunci ba ya hawa kan su.

2 – Kashi 80% sun hakkake cewa gwamnati ba ta yi wa kabilar su adalci. Ana tauye su, ana fifita wata ko wasu kabilun.

3 – Kashi 74% na ganin cewa ba a yi wa addinin su adalci, ana tauye su.

4 – Kashi 4 bisa 10 ne kadai suka yi amanna da Shugaba Muhammadu Buhari.

5 – Kashi 55% ke tutiya da kasancewar su ‘yan Najeriya.

6 – Kashi 30% na yin tir da yadda Najeriya ta tsinci kan ta a halin yanzu, tare da nuna rashin gamsuwar su da gwamnati.

A takaice, wannan bincike ya tabo bangaren gamsuwa da Majalisar Tarayya da ta Dattawa, kaunar juna, da-na-sanin kasancewa ‘yan Najeriya, kai har ma da batun bukatar canja wata kasa.

Hakan ya tabbatar da cewa kawunan ‘yan Najeriya ba a hade su ke ba. Sannan kuma kishin kasa da kaunar juna sun yi karanci sosai a zukatan ‘yan Najeriya.

Share.

game da Author