Bashin da bankuna ke bai wa manoma bai wuce kashi 4 bisa 100 ba

0

Humumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta nuna damuwar cewa har yau bashin da bankunan kasuwanci ke bai wa manoma bai wuce kashi 4 bisa 100 na yawan basussukan da suke bayarwa ba.

NBS ta kafa hujja ne da bayanin kididdigar alkaluman da Babban Bankin Najeriya, CBN ya bai wa hukumar, cewa daga watan Mayu zuwa Agusta na 2019, kashi 4 cikin 100 na bashin da bankuna suka bayar ne kadai aka bai wa manoma.

NBS ta ce bankuna sun bayar da bashin naira tiriliyan 15.1 cikin wadannan watanni hudu na tsakiyar 2019.

Sannan kuma kididdigar ta kara yin nuni da cewa babu wani bambanci tsakanin basussukan da bankunan suka bayar daga Janairu zuwa Afrilu, da kuma Mayu zuwa Augusta, 2019.

A watanni hudun farkon shekara bankuna sun bayar da bashin naira tiriliyan 15.2 , amma naira bilyan 638 ce kadai ta tafi a harkokin noma.

Masana’antu da ayyukan gudanarwa ne suka fi cin moriyar bashin, inda a farkon watanni hudun 2019 aka bai wa masana’antu kashi 40.27 na yawan bashin, a watanni hudu na Mayu zuwa Agusta kuma suka bashin kashi 39.60.

Sauran ayyuka sun samu na kashi 53.53 na farkon shekara, sai kuma kashi 56.20 a tsakanin Mayu da Agusta.

CBN dai ta nuna damuwar cewa duk da tsarin bai wa manoma ramcen kudade na ‘Anchor Burrowers Program da ta shigo da shi, har yau manoma na a sahun baya wajen karbar basussukan inganta harkokin noma.

Share.

game da Author