Bankin DBN ya bai wa masu kananan masana’antu 95,000 ramcen naira bilyan 100

0

Bankin Raya Kasa na ‘Development Bank of Nigeria, ya bayyana cewa a cikin shekarar 2019 da ake ciki, ya bada lamuni na zunzurutun kudade har naira bilyan 100 ga masu kananan masana’antu su 95,000.

Manajan Daraktan na DBN, Tony Okpanachi, ya ce an bayar da basussukan ne ga kanana da matsakaitan masana’antu ne inganta su a cikin kasar nan.

Ya yi wannan albishir ne ranar Talata, a Maiduguri, yayin da ya ke jawabi ga mahalarta Taron Yadda Za a Saukaka Wa Masu Kananan ‘Masana’antu Hanyar Samun Ramce

An gudanar da taron a Fadar Gwamnatin Jihar Barno, a Maiduguri, inda Gwamna Babagana Zulum ya karbi bakuncin mahalarta taron, wanda shi ne irin da na farko.

Ya ce an bayar da wannan lamuni ga mutane ko kuma kananan da matsakaitan masana’antu 95,000 a cikin jihohin kasar nan.

Okpanachi ya kara da cewa ko a cikin shekarar 2018 sai da aka raba lamunin naira bilyan 30 ga masu kananan masana’antu har 35,000.

Ya ce akasarin wadanda aka ba lamunin, kashi 72 bisa 100 mata ne. Yayin da kashi 51 bisa 100 din su kuma matasa ne.

An bayar da lamunin a karkashin Kunguyoyin NACCIMA, SMEDAN, Jami’o’i da sauran cibiyoyin hada-hadar kasuwanci.

Okpanachi ya ce akwai bukatar a rika bayar da lamunin domin inganta tattalin arziki, kasancewa akwai masu kananan masana’antu hat milyan 41.5 a kasar nan, wadanda da yawan su ba su samun damar karbar lamunin.

Share.

game da Author