Jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, ta daukaka karar hukuncin da Kotun Daukaka Karar Zaben Gwamna.
Da ya ke jawabi a wurin taron manema labarai jiya Talata a Bauchi, Shugaban APC na jihar, Uba Nana, ya ce ya zama wajibi su daukaka kara zuwa gaba, domin ba su gamsu da hukuncin da kotu ta yanke a ranar Litinin ba.
Ya ce ya na da yaki ni da kuma fatan samun adalci a kotun gaba. Daga nan ya yi kira ga dukkan ‘yan jam’iyyar APC a fadin jihar Bauchi cewa kada hukuncin da kotu ta yanke ya kashe ko sanyaya musu guiwa.
Ita dai Kotun Daukaka Karar Zaben Gwamna ta kori karar da APC da dan takarar ta suka shigar domin neman soke zaben da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya yi nasara.
APC da dan takarar ta, tsohon gwamna, Mohammed Abubakar sun garzaya kotu, amma kuma a jiya kotu ta kori karar ta su.
Shugaban Alkalan, Salihu Sha’aibu, ya ce babu wata hujja cikakkiya da kotu za ta gamsu da ita cewa Bala bai ci zabe ba.
Sun yi ja-in-ja ne a kan zaben Kananan Hukumomin Tafawa Balewa da kuma Bogoro. A kan wannan ma kotu ta ce Bala ya yi nasara fintinkau.
Baya ga korar karar da aka yi, an kuma ci tarar APC naira 300,000, kudin da aka ce za ta biya PDP, Gwamna Bala da kuma INEC naira 100,000 kowanen su, saboda ta bata musu lokacin zirga-zirga a kotu.
Haka nan kuma jiya wata Kotun Daukaka Karar Zaben ta kori karar da APC ta shigar inda ta kalubalanci nasarar Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai.
Da wannan nasara da Ortom da kuma Bala Mohammed suka samu a kotu a jiya, wadannan shari’u na Zaben gwamna gaba daya da aka yanke hukunci a Najeriya, sun nuna babu inda masu adawa suka yi nasara a kotu.
Gaba daya gwamnonin APC da aka maka kotu, babu wanda aka kayar. Haka a bangaren PDP ma babu wanda kotu ta jijjiga kujerar mulkin sa.
Discussion about this post