Fitaccen dan wasan fina-finan Hausa Jarumi Ali Nuhu ya samu karrama daga daliban Najeriya dake Kasar Indiya.
Daliban sun gayyace jarumi Ali ne domin bikin ranar ala’adu ada ake yi a kasar duk shekara ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba.
A wajen bukin an saka wa Jarumi Ali Nuhu kayan kwalliya irin na mutanen indiya sannan kuma har an kalli wasu daga cikin fina-finan da jarumin yayi na Kannywood.
Ali Nuhu ya tattauna da jaridar BBC Hausa inda ya ya bayyana jin dadin sa game da wannan karramawa da daliban Najeriya dake kasar Indiya su ka yi masa.
” Daliban na karanta fanni daban-daban kama daga fannin likita zuwa hada magunguna da injiniya da dai sauransu. Sannan wasu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe ta ke.” Inji Ali Nuhu.
Hassana Dalhat da ta tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA, inda ta bayyana cewa ko shakka babu Ali Nuhu ne ya fi yin zarra a harkar fina-finai a Arewacin Najeriya sannan kuma daya daga cikin jaruman Arewacin Najeriya da suke gogawa da takwarorin su na Nollywood.
” Ali Nuhu ya kwana biyu a harkar fina-finan Hausa sannan ya yi matukar raya farfajiya. Ali ya goya wasu fitattun ‘yan wasa kamar Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi, Nuhu Abdullahi da sauran Jarumai da suka yi fice a farfajiyar.
Wannan Karrama da ya samu yana daga cikin daruruwa da ya rika samu a cikin sama da shekaru 30 a harkar shirya wasan kwaikwayo.