An tsinci gawar wani babban soja a Abuja

0

A safiyar Talata ne aka tsinci gawar wani babban Soja mai mukamin ‘2nd Lt’ a kusa da karkashin gadan unguwar Mabushi dake Abuja.

An tsinci gawar Sojan mai suna VL Henry kwance lullube da rigarsa na soja duk an sassare shi.

Babu wanda ya bada takamammen bayani game da abinda ya faru da har aka rasa wannan Sojan.

Wani Soja da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya bayyana cewa akwai yiwuwar cewa wasu ne suka farwa Sojan a wannan unguwa, ko yan daba, barayi ko ‘yan kwace.

Tuni dai har an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa dake Asibitin Abuja.

Rundunar Soji ta gargadin sojoji da su rika yi su suna ankarewa sannan idan da hali su rika tafiya su biyu ko ma fiye.

Babban birnin tarayyan Najeriya da ake tunkaho da ita a da wajen tsaro da zaman lafiya na neman ya zama fa shiga da alwalanka.

Domin kuwa rahotanni da ake samu musamman a dan kwanakin nan suna nuna yadda ayyukan ‘yan ta’adda, yan iska da ‘yan daba ke neman ya gurgunta tsaro da zaman lafiyan da ake tunkaho da su a babban birnin.

A kusan kullum sai kaji an yi wa wani kwace, fashi ko kuma an yi garkuwa da wani ko wata.

Abin dai ya dade yana ci wa mutane musamman mazauna garin tuwo a Kwarya.

Share.

game da Author