An dawo da ‘tollgates’ domin karbar haraji hannun direbobi a manyan titunan kasar nan

0

Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar cewa ta dawo da shingayen karbar kudaden haraji a hannun direbobi da dukkan matuka motoci a kan manyan titinan gwamnatin tarayya a fadin kasar nan.

Jiya Laraba ne Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola ya bayyana wa ‘yan jaridar Fadar Gwamnatin Tarayya haka.

Ya yi musu bayanin j kadan bayan tashi daga taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Fashola ya ce a wurin taron ne Buhari da sauran ministoci suka amince da gaggauta dawo da karbar kudaden, wadanda gwamnatin baya ta soke karba, sama da shekaru goma da suka gabata.

Sannan kuma Fashola ya ce dama tuni ba tun yau ba an rigaya an ma zana taswirar zanen yadda ginin shingayen na ‘tollgates’ za su kasance. Kuma ya kara da cewa za a fadada wurin karbar kudaden yadda a a samu akalla wurare goma na kudade a kowace ‘tollgates’, domin magance cinkoso.

Da ya ke bayanin kare wannan sabon tsarin karbar haraji da gwamnatin su ta dawo da shi bayan soke shi da wata gwamnati ta yi, Fashola ya ce “wata gwamnati ta soke karbar kudaden, amma kuma babu wata doka da ta haramta wa wata gwamnati ta sake dawo da tsarin.”

Ya ci gaba da cewa ana kokarin hada kai da bankuna ta yadda za a saukaka karbar kudaden da tara su da kuma kauce wa harkalla. A nan ya yi wani nuni da ke nuna cewa ba su kudi mai mota zai rika mikawa a ‘tollgates’ ba. Ya ce ta hanyar ‘mobile banking’, wato tsarin hada-hadar zamani za a rika karbar kudaden.

Hakan na nufin da ATM direba zai rika biyan kudi kenan, ko kuma wata dabarar za a bijiro da ita daban.

Ga misalin yadda direbobin motoci na haya ko na gida za su rika biyan kudaden.

1. Kano-Abuja

Za ka biya kudi a fita Kano.

2. Sai ka biya a shiga Zaria.

3. Za ka biya a shiga Kaduna.

4. Sai ka biya a fita Kaduna.

5. A shiga Abuja sai ka biya.

Da ATM direba zai rika biya, ba da takardun kudi ba.

Yadda ka biya a wurare 5 idan za ka tafi, haka sai ka biya a wurare 5 idan za ka dawo.

Share.

game da Author