Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta sanar da kubutar da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda da masu garmuwa suka sace a Kaduna.
Idan ba a manta ba, ranar Asabar ne masu garkuwa suka tafi da mataimakin kwamishinan ‘Yan sanda Musa Rambo a hanyar sa ta zuwa garin Jos.
Rambo kamar yadda ale kiransa da shi ya fada hannun masu garkuwa ne a a daidai yana iyakar Kaduna da Nasarawa, a kusa da dajin Kanock.
An tsinci motarsa da ‘ID Card’ din sa a cikin motan.
Tun a ranar Asabar dinne rundunar ‘Yan sandan suka fantsama neman wadanda suka sace Rambo da kuma kubutar da shi.
Yadda aka sace Kwamishina Rambo
Masu garkuwa da mutane sun sace mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa Rambo a hanyar sa ta zuwa garin Jos a iyakar Kaduna da Nasarawa.
Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya bayyana wa manema labarai cewa, an tsinci motar mataimakin kwamishina Rambo ne a kusa da Jos daidai dajin Kanock.
An ajiye motar a gefen titi, sannan aka ajiye Katin shaidar sa na ma’aikaci a cikin motar, wato ID card.
A wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, ta ce zuwa yanzu maharan sun kira ‘yan uwan kwamishina Rambo suna bukatar a biya naira miliyan 50 kudin fansa.
Sai dai kuma Sabo ya ce tuni har ‘yansanda sun fantsama danin Kanock domin farautar wadannan mahara da kuma ceto mataimakin kwamishina Rambo.
Sannan bai ce komai ba game ko maharan sun nemi abiya kudin fansa ko a’a.
Discussion about this post