Kwamitin da gwamnatin jihar Zamfara ta kafa domin kirkiro matakan da za a bi don kawar da matsalar hare-haren mahara da garkuwa da mutane ta gano cewa masu garkuwa da mutane sun karbi wuri na gugan wuri har Naira biliyan uku daga ‘yan uwan mutanen da suka yi garkuwa da su a jihar.
Shugaban kwamitin Mohammed Abubakar ya bayyana haka da yake mika rahotan kwamtin sa ga gwamna Bello Matawalle a garin Gusau.
Abubakar yace ‘yan uwan wadanda aka yi garkuwa da da mutane sun biya wadannan kudaden ne tsakanin watannin Yunin 2011 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2019 kudin fansan ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su har 3,672.
Ya kuma kara da cewa mata 4,983 ne suka rasa mazan su,yara 25,050 sun rasa iyayensu sannan mutane 190,340 sun rasa gidajen su na zama.
An sace wa Fulani makiyaya shannu 2,015,tumaki 141,awaki,jakuna da rakuma 2,600 sannan an kona motoci da Babura 147,800 duk a tsakanin wannan lokaci.
Cikin shawarwarin da kwamitin ta bada kwai shawarar a yi kotu da zai rika shiga tsakanin wadanda ba su jituwa musamman manoma da makiya.
Sannan kuma da gwamnati ta hada hannu da gwamnatocin dake makwabtaka da ita domin a iya kawo karshen wannan mummunar abu da ya addabi mutane.
A kashe gwamna Matawalle ya yabawa kwamitin da aikin ta yi. Ya ce lallai gwamnati za ta duba rahoton kwamitin kuma zata yi amfani da su.