Amurka za ta dawo wa Najeriya da Naira Biliyan 108 Kudin Abacha

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa gwamnatin Amurka zata mika wa Najeriya Naira biliyan 108 kudin dake wani asusun ajiya a kasar wanda Abacha ya wawura.

Buhari ya bayyana haka ne a jawabin da yayi wa ‘Yan Najeriya ranar Talata, ranar da Najeriya ta cika shekara 59 da samun ‘yancin kai.

Shugaba Buhari ya ce tuni har an kusa cimma matsaya game da yadda za a mika wa Najeriya kudin.

” Ma’aikatar shari’a na Najeriya da na kasar Amurka suna ci gaba da tattaunawa game da yadda za a mika wa Najeriya wannan kudi.

Bayan haka kuma muna ci gaba da tattaunawa da wasu hukumomin gwamnatin kasashe domin kwato kudaden Najeriya da aka boye a kasashen su. Sannan kuma na saka hannu a wata kudiri da ya zama doka yanzu domin hukunta mutanen da aka samu da hannu a aikata irin wannan aiki.

Dokar zai kara wa jami’an tsaro karfi da basu damar yin binciken koma wanene aka samu da hannu a harkallar kudin gwamnati.

Share.

game da Author