Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ce komawa yin amfani da kayayyakin da aka sarrafa a nan Najeriya ne kadai za su magance mana matsalolin da ke addabar kasar nan.
Ya yi wannan bayanin a lokacin da ya ke bude taron Bunkasa Tattalin Arziki na 25, wato (NES25) a Abuja.
Buhari ya yi kira ha Shugabannin bangaren masana’antu masu zaman kan su da na gwamnati su lalubo hanyar dogaro da kan mu, ta yadda za mu fi tsayawa kan kafafun mu da kan mu idan ana maganar tattalin arziki.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da bada hadin kai domin inganta masana’antu a cikin gida ta yadda tattalin arzikin mu zai inganta.
“An sanar da ni cewa wannan taro zai maida hankali ne wajen inganta noma, ICT, wato fasahar zamani, masana’antu da kuma fadada jarin ganin an samu ci gaban da sai kayan gida ne kawai zai kawar mana da kalubale da matsalolin da suka dabaibaye mu.
Da ya karkata kan zaben 2019, Buhari ya ce ya yi farin ciki ganin cewa masu jayayya da sakamakon zabe sun garzaya kotu, ba su fita kan titina zu ka kone-kone ba.
Ya ce hakan na nuni da cewa dimokradiyya ta zauna daram da gindin ta.
“Gudanar da zabe lami lafiya shi ma ci gaban dimokradiyya ne, in banda wasu ‘yan wuraren da aka yi hatsaniya.
Da Buhari ya sake juyawa kam tattalin arziki da rayuwa, ya ce ” wasu manazarta kan yi kuskuren gwamutsa ma’anar yalwar arziki da dukiya. Buhari ya ce dukiya ita ce kudi.
“Yalwar arziki kuwa, to irin rayuwar da al’ummar kasa ta zabar wa kan ta, ta ke tafiya a kai, kuma sahihiyar rayuwa ba ta hauma-hauma ba.”
Daga nan ya fito fili ya ce jihohi 4 ko 5 ne kadai a kasar nan ake rayuwa a cikin yalwar arziki. Da kuma Abuja. Sai kuma dukkan wadanda ke cikin wannan dakin taro, su ma su na cikin masu rayuwa cikin yalwar arziki.”
“Amma sauran jihohi 31 da ke dauke da yawan al’umma milyan 150, duk rayuwa ce ake yi ta jiran-gawon-shanu da ya-mu-samu-ya-mu-sa-bakinmu.”
Da ya koma kan kirdadon cewa nan da 2050 yawan ‘yan Najeriya zai iya kai milyan 400, Buhari ya ce gwamnati kan turbar dora kowa kan yin riko da duk irin damar da ya samu, kada ta kubce masa.
Ya ce ana ci gaba da inganta fannin ilmi, lafiya, noma, ayyukan raya kasa, tsaro da sauran su.