Alkalan Kotun Koli ma na iya yin kuskure – Babban Jojin Najeriya

0

Babban Jojin Najeriya, Ibrahim Muhammad, ya bayyana ce su ma alkalan Kotun Koli ‘yan Adam ne, za su iya yin kuskure, idan kuma sun yi kuskuren, ba abin mamaki ba ne.

Cikin wani jawabi da ya fitar, wanda Daraktan Yada Labarai na Kotun Koli, Festus Akande ya sa wa hannu, Muhammad yay i wannan tsinkayen ne ranar Talata a Abuja.

Babban Jojin ya yi wannan bayani ne a lokacin da Shugabannin Hukumar AMCON suka kai masa ziyara.

“Idan aka yi la’akari da irin yadda mu ke aiki, idan akwai wani daga cikin ku da ke da wani gyara ko korafi ko tsinkaye, to zai iya rubuto mana, ya soki irin aikin mu ta irin yadda ilmin ku da gogewar ku ya suka nuna muku.

“Mu ba mu ce mun san komai ba. Har yanzu koyo mu ke yi. Mu na ci gaba da koyo, kuma mu na samun ilmin abin.

“Kofar mu a bude ta ke a rika sukar aikin mu idan akwai abin sukar. Kai ko da lugga ko rubutun mu, ko aya ko wakafi da sauran su duk za a iya gyara mana, domin kauce wa kuskure a hukunce-hukuncen da mu ke yankewa.”

Ya ce masu shari’a ba su jin haushi ko ganin laifin wanda duk ya ci su gyara. Musamman ya ce a wuraren da su ke yin kuskuren nahawu da balagar Turanci.

Ya ce wannan bayani da ya yi, haka ya ke har a Kotun Daukaka Kara da Kotun Tarayya, domin ganin cewa hukunci ya tafi daidai da daidai, yadda za a rika kauce tafka kura-kurai.

Daga nan sai ya kara da bayanin cewa duk wani alkalin da ya san abin da ya ke yi, dole ya rika hakuri da juriyar karbar gyara. Kada ya ce shi ai ya san komai, ba ya kuskure.

“Sai dai kuma ba a tirsasa alkali, ko yi masa barazana ko matsa masa lambar ya bi ra’ayin wani wajen yanke hukuncin sa.” Inji shi.

Share.

game da Author