A daina nuna wa matan da basu haihuwa kiyayya – Kiran Aisha Buhari

0

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga kasashe Afrika da su daina nuna wa matan da basu haihuwa kiyayya karara cewa yin haka bai dace ba.

Ta ce nuna kiyayya ga matan da bata haihuwa babban matsala ne dake iya jefa ta cikin damuwa, kunci da tabuwar hankali.

Aisha ta fadi haka ne a taron tattauna matsalolin da ake fama da su wajen inganta fannin kiwon lafiya a kasashen Afrika da aka yi Accra , Bababn Birnin Kasar Ghana.

Wannan taro da shine karo na shida da kungiyar ‘MERK AFRICA-ASIA LUMINARU/MORE THAN A MOTHER INITIATIVE’ take shirya an yi shi domin tattauna irin gudunmawar da matan shugabannin kasashen Afrika ke yi wajen inganta lafiyar mata da yara kanana.

Aisha ta ce matsalar rashin haihuwa abu ne dake iya faruwa da kowa.

Daga nan Aisha ta ce ta kafa wasu gidauniya har biyu wato ‘Aisha Buhari Foundation (ABF)’ da ‘Future Assured Programme’ domin inganta rayuwar mata a Najeriya.

Gidauniyar sun horas da mata sana’o’in hannu da samar musu kudaden jari sannan ta taimaka wa matan da basu haihuwa 200.

Aisha ta ce ta kuma gina asibitocidomin kula da mata a mazabu a kasar nan tana mai cewa zata ci gaba da gina wasu.

Share.

game da Author