ZANGA-ZANGA: Yadda ‘Yan sanda suka tarwatsa ‘yan shi’ a titunan Abuja

0

A ranar Juma’a ne dakarun ‘yan sanda a Babban Birnin tarayya Abuja suka tarwatsa gungun wasu masa ‘yan shi’a da ke zanga-zangar nuna soyayya ga jikan manzon Allah da Hussain RA da kuma kira da a saki El-zakzaky.

‘Yan shi’an sun artayo unguwanni Wuse a daidai an idar da sallar Juma’a. Nan da nan kuwa ‘Yan sanda suka fatattake su suna jejjefa barkonun tsohuwa sannan suna harbi sama.

Masu zanga-zangan suna ta kowa suna fadin “Labbaika yah Hussein. A saki Zakzaky”.

‘Yan sanda sun rika jefa barkonun tsohuwa domin tarwatsa wadannan matasa.Mutane da mazauna unguwannin Wuse Zone 3 da Zon 2 sun rika arcewa da gudu suna kulle gidajen su. Masu mota kuma suna ta jujjuya motocinsu domin canja hanya.

Idan ba a manta ba a watan Yulin da ya gabata ne ‘yan shia mazu zanga-zanga suka gwabza da jami’an tsaro a Abuja inda arangamar yayi sanadiyyar konewar wasu motoci na mutane da na gwamnati da dama.

‘Yan shia sun fito zanga-zangar ci gaba da kira da suke yi ga gwamnati da ta saki shugaban su Ibrahim El-Zakzaky dake tsare tun a shekarar 2015.

Sun faro zanga-zangar ne daga mahadar Nitel inda suka dunguma zuwa Sakatariyar Abuja. A hanya suna Kabarbari suna cewa Allah ya kashe shugaban Amurka Trump, Allah ya kashe Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A daidai sun Iso Sakatariyar ne sojoji suka nemi tsaida su amma hakan bai yiwu ba daga nan sai aka fara batakashi a tsakanin su

Share.

game da Author