‘Yan Najeriya sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da ziyarar kasar Afrika Ta Kuda da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, Gwamma Ekiti Kayode Fayemi da Sarkin Kano Sanusi Lamido duk da Allah wadai da ake yi wa ‘yan kasan saboda kashe ‘yan Najeriya da suke yi.
An rika yada hotunan su a kasar Afrika Ta kudu duk cewa ‘yan Najeriya na cike da fushi bisa ga kashe kashen da ‘yan kasar ke yi wa ‘yan Najeriya da baki.
Sai dai kuma ‘yan Najeriya sun yi tir da wannan ziyara na gwamnonin suna masu cewa wadannan gwamnoni basu kyauta ba ganin cewa hatta gwamnatin tarayya sun janye da ga halartar taraon WEF da akeyi a kasar domin nuna fushinsu ga yadda ake cin zarafin ‘yan Najeriya a kasar.
Sai dai Fayemi yace ba su ziyarci Kasar Afrika ta kudu bane domin su halarci taron WEF, wani abu ne dabam ya kaisu kasar. Ya kara da cewa wani babban abokinsa ne ya gayyace sa wani buki can da ban ba ma a jihar da ake yin wannan taro ba.
Sai dai El-Rufai da Sarkin Kano basu ce komai game da wannan ziyara da ake ta cece-kuce akai ba da kuma yin tir da shi ba.
Idan ba a manta ba ita ma tsohuwar ministan Ilimi Oby Ezekwesili ta banzatar da kiraye kirayen da aka yi ta yi na kada a ziyarci kasar inda ta garzaya taron a kasar Afrika Ta Kudu.
Ita ma fitacciyar ‘yar jarida, Kadariya Ahmad wadda da ita ce aka tafi wannan kasa da ta ce sun kai kusan kwanaki 7 a kasar, kuma babu abin da ya hada su da taron WEF.
Tace ta fito ne domin yin bayani ga ‘yan Najeriya domin su san gaskiya game da abin da yake faruwa da kuma dalilin ziyararsu kasar Afrika ta Kudu din.