Majalisar dokoki ta kasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da da magungunan zazzabin cizon sauro kyauta a duk asibitocin gwamnati dake kasarnan.
Majalisar ta kuma yi kira ga kwamitin kiwon lafiya da ta hada hannu da ma’aikatar kiwon lafiya, hukumomin kiwon lafiya da kungiyoyin bada tallafi domin ganin an samun nasarar dakile yaduwar zazzabin cizon sauro a Najeriya.
Bem Mzomdu (PDP) dake wakiltar jihar Benuwai wanda shine ya jagoranci muhawarar a zauren majalisar ya koka da halin da Najeriya ke ciki game da zazzabin cizon sauro.
Mzomdu ya ce duk shekara mutane miliyan 100 a Najeriya na kamuwa da zazzabin cizon sauro.
Ya kuma ce kashi 50 bisa 100 na matasan kasar nan kan kamu da wannan cuta akalla sau daya a shekara sannan yara ‘yan kasa da shekara biyar kuwa kan kama cutar sau biyu zuwa hudu a shekara.
“Idan ba a manta ba a 2005 Najeriya na daya daga cikin kasashe 15 daga Kudancin Saharan Afrika da cibiyar ‘President’s Malaria Initiative (PMI)’ ya tallafa wa don yaki da cutar.
“Tallafin ya hada samar da kula da magunguna wa mata masu ciki, yi wa mutane gwajin cutar da samar da magungunan da suke bukata sannan da raba gidajen sauro da yin feshi domin dakile yaduwar cutar.
“Bayan haka a taron kasashen Afrika da aka yi a Abuja a shekarar 2005 gwamnatocin kasashen Afrika sun yi alkawarin ganin cewa kashi 60 bisa 100 na mutanen dake zama a wuraren da aka fi kamuwa da cutar suna samun kula.
“Tsarin tallafin PMI na shekarar 2015 zuwa 2020 ya nuna cewa Najeriya kan yi asaran Naira biliyan 132 a dalilin wannan cuta. Sannan kuma kashi 76 bisa 100 na adadin yawan mutanen dake kasarnan suna zama ne a wuraren da aka fi yawan kamuwa da zazzabin cizon sauro’’.
Mzomdu ya ce duk da daukan matakan hana yaduwar cutar da kudaden da gwamnati ke kashewa har yanzu tallakawa basu iya siyan magungunan cutar.
Ya ce domin haka ya kamata gwamnati ta samar da maganin cutar kyauta a duk asibitocin gwamnati dake kasar nan domin tallafa wa talakawa.
Discussion about this post