ZABEN 2019: Rashin tabukawar da mata suka yi abin damuwa ne -INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya bayyana damuwar hukumar dangane da rashin damawar da ba a yi da mata sosai a siyasar 2019 ba.

Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa baya ga rashin yawaitar mata shiga takarar zabe, hatta a wajen jefa kuri’a ma ba ta ba su fito kamar yadda aka yi zato ba.

Yakubu ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a, wurin taron bitar yadda Zaben 2019 ya kasance.

Da ya ke jawabi, wanda ya wakilci shugaban na INEC, wato Adekunle Ogunmola, ya ce dukkan kokarin da INEC ta yi wajen wayar da kan mata da su shiga a dama da su, bai shiga kunnuwan matan yadda ake so ba.

Ya ce irin fitowar da mata suka yi domin fafatawa a zaben 2019, ba ta yi armashi ba, domin abin da tsarin daidaito ya nuna shi ne a bai wa mata damar akalla kashi 35 bisa 100.

Sai dai kuma ya yi hasashen cewa akwai matsaloli ko dalilan da su ka haddasa rashin tabukawar da matan suka yi. Ya ce yawancin su ba a kan mulki su ke ba, sannan kuma akwai rashin kudade tare da su.

A bayanin sa, ya ce mata da dama sun fito takara, amma yawanci ba su yi nasara a zabukan fidda-gwani ba saboda zabukan sun zo da rudani da giribtu da kuma hauma-hauma.

Ya ce an samu mata a takarar shugaban kasa su 5 kadai, daga cikin ‘yan takara 73. Sannan mata 232 daga cikin masu takarar sanata 1,665.

A takarar majalisar tarayya kuwa, mata 533 aka samu daga cikin masu takara 4,139. Yakubu ya ce an samu mata 7 sanatoci daga cikin 109. Sai kuma mata 11 a Majalisar Tarayya daga cikin mambobi 390.

Babu mace gwamna, amma an samu mata 4 a mukamin mataimakin gwamna.

Yakubu ya ce INEC ba za ta gajiya ba, za ta ci gaba da tunatar da mata domin shiga a dama da su.

Share.

game da Author