Dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya garzaya Kotun Koli, inda ya daukaka karar shari’ar da Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta jaddada wa Shugaba Muhammadu Buhari nasarar da ya samu a zaben 2019.
Daya daga cikin manyan lauyoyin Atiku, wato Mike Ozekhome, ya bayyana wannan daukaka kara zuwa Kotun Koli da ya ce sun yi a kan dalilai 66.
A kan wadannan dalilai ne ya ce ya yi amanna alkalan Kotun Daukaka Kara da suka bai wa Buhari da APC nasara, sun dibga kuskure a hukuncin da suka yanke.
A ranar 11 Ga Satumba ne Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa, a karkashin Shugabancin Babban Mai Shari’a Mohammed Garba, ta bai wa Buhari da APC nasara a kan Atiku da PDP.
Kotun ta ce Atiku da PDP sun kasa gabatar da hujjojin da za su gamsar da kotun har ta gamsu da cewa an yi wa Atiku magudi, kuma shi ne ya yi nasara, kamar yadda Atiku da PDP din suka nemi kotun ta zartas.
A na sa bangaren, lauya Ozekhome bai lissafa dalilai ko hujjoji 66 da ya ce sun gabatar wa Kotun Koli ba.
Sai dai kuma wasu daga cikin batutuwan ba za su rasa hadawa da batun a soke takarar Buhari ba da kuma batun zargin runbun adana bayanan kididdigar zabe na server da Atiku ya yi ikirarin ya ga sakamakon da ya nuna shi ne ya yi nasara a ciki.
INEC dai ta karyata Atiku, haka nan kuma kotun Daukaka Kara ta ce Atiku ya kasa kawo hujja gamsassshiya cewa akwai ‘server’ din.
Batun takardar shaidar sakandare na Buhari da Kotun Daukaka Kara ta zartas da hukunci a kai, ya jawo cece-ku-ce a fadin kasar nan. Kuma har da shi Atiku da Buhari suka hada suka sake daukaka kara zuwa Kotun Koli.
Discussion about this post