ZABEN 2019: APC ita ma ta daukaka kara hukuncin shari’a zuwa Kotun Koli

0

Jam’iyyar APC ta shigar da sabuwar kara a Kotun Koli, inda ta ke jayayya da wasu sassan da Kotun Daukaka Kara ta ba dan takarar PDP, Atiku Abubakar gaskiya, duk kuwa da cewa an kori karar da Atiku ya shigar daga karshe.

APC ta shigar da karar ce jiya Talata, inda ta nemi Kotun Koli ta yi watsi da wasu shaidu da Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta karba daga bangaren Atiku.

Tun ranar Litinin ne Atiku da PDP suka shigar da daukaka kara a Kotun Koli, inda su ke kalubalantar hukuncin da Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta yanke cewa Atiku da PDP sun kasa gabatar da kwararan hujjojin da za su gamsar cewa an yi musu magudi a zaben 2019.

PDP da Atiku sun bayyana wa Kotun Koli cewa alkalan Kotun Daukaka Kara sun tabka shirme da suka ce wai dan takarar zaben shugaban kasa na APC, Buhari ba sai ya gabatar wa INEC da satifiket na kammala makaranta ba, kamar yadda doka ta wajabta a yi a cikin fam na INEC mai lamba CF001.

Akwai sauran hujjoji har 65 da PDP suka gabatar wa Kotun Koli, wadanda suka nuna wa kotun cewa Kotun Daukaka Kara ba ta yi musu adalci ba, kamar yadda suka yi ikirari.

A na ta bangaren, APC ta shigar da karar cewa kada Kotun Koli ta yi amfani da bayanai da hujjojin da masu gabatar da shaida na PDP mai lamba 40, 59 da 60 suka gabatar a Kotun Daukaka Kara.

Daga cikin shaidar da APC ta nemi kada Kotun Koli ta yi amfani da su, har da shaidar da kakakin PDP, Segun Showunmi ya gabatar, wanda shaida ce ta wani faifan bidiyo da aka nuno daya daga cikin jami’an INEC na Jihar Bayelsa, Mike Igini ya na bayani a gidan talbijin, inda ya ke ikirarin cewa INEC za ta tattara bayanan zabe a cikin rumbun ajiyar sakamakon kididdigar yawan kuri’u, wato server.

Akwai kuma shaidar da mai shaida na 59 David Njorga da na 60 Joseph Gbenga suka gabatar a bangaren PDP, wadanda duk masana kulumboton harkar kwamfuta ne.

Bayan wannan kuma, APC na bukatar Kotun Koli ta yi watsi da wasu bayanai masu yawan sadara 42 daga abin da PDP ta gabatar ma ta.

Wadannan bukagtu da APC k enema daga Kotun Koli, duk daya daga manyan lauyoyin ta, Leteef Fagbeyi ne ya gabatar da su.

Kotun Koli dai ba ta bayyana ranar fara sauraren kararrakin ba.

Share.

game da Author