Za mu ci gaba da tallafa wa Mata da dabarun bada tazarar iyali – MSION

0

Kungiya mai zaman kan sa Mai suna ‘Marie Stopes International Organinsation Nigeria (MSION)’ ta yi kira ga gwamnatocin duniya da su wadatar da dabarun bada tazarar iyali ga duk matan dake bukata.

Shugaban kungiyar MSION Effiom Effiom ne ya yi wannan kira a taron bukin ranan amfani da dabarun bada tazaran iyali a Abuja.

A taron na bana mai taken ‘Rayuwar kine kuma hakkin ki ne’ an tattauna yadda za arika wayar wa Mata Kai game da ingancin bada tazarar iyali.

Effiom ya ce wayar da kan mata ya zama dole ganin cewa har yanzu mata miliyan 214 dake bukatan dabarun bada tazaran iyali basu iya Kai has shi.

Effiom yace domin samar da tallafi kungiyar su na bai wa matan dake bukata dabarun bada tazaran iyali kyauta a Najeriya.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen samun matan da za su iya kammala karantun boko,mata masu koshin kiwon lafiyar da za su iya taimakawa wajen inganta tattalin arzikin kasa.

Share.

game da Author